Ƙarni na 21 ya zama zamanin rikice-rikice — Shugaban ƙasar Turkiyya

Tsarin da duniya ke amfani da shi a halin yanzu, wanda ba shi da adalci da bin gaskiya, ba zai haifar mata da ɗa mai ido ba, in ji shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

Yayin da yake jawabi a wurin taro kan diflomasiyya wato Antalya Diplomacy Forum (ADF), wanda aka soma a birnin Antalya da ke gaɓar Tekun Rum a ranar Juma’a, shugaban na Turkiyya ya ce yaƙe-yaƙen da ake yi a Syria, Yemen, Libya, da Ukraine sun nuna cewa tsarin da ake amfani da shi a duniya a halin yanzu ya gaza samar da mafita.

“Ƙarni na 21 ya zama zamanin rikice-rikice ba kamar yadda aka yi zato ba, inda aka gaza samun tsarin duniya mai adalci don haka iƙirarin samar da adalci ya zama kawai ‘wani take,” a cewar Erdogan.

Bayyana yadda rikicin Gaza yake kasancewa kaɗai ya isa fahimtar irin yadda tsarein duniya ke rugujewa, Shugaban Ƙasar Turkiyyan ya ce “Abin da ke faruwa a Gaza ba rikici ba ne kawai, ƙoƙari na kisan kiyashi – saboda ko yaƙe-yaƙe ma suna da nasu dokokin.”

A yayin da yaƙin da ake yi a yankin Gaza na Falasɗinu ya shiga kwana na 147, Shugaban Ƙasar Turkiyya ya nuna yadda ake yi wa yara da mata da fararen hula kisan gilla a Gaza.

Ya kuma yi bayani a kan yadda lamarin ke daƙusar da imani da yardar da mutane suka yi da adalaci da tsarin duniya.

“Ina magana ne game da hari na yaudara da rashin mutunci da rashin mutunci da ake yi.”

Da yake sukar tsarin da ƙasashen duniya ke ciki a halin yanzu da kuma masu mara wa Isra’ila baya, ya ce “Masu ƙarfi na Yammacin Duniya da suke goyon bayan Isra’ila ba tare da wani sharaɗi ba tun da farko suna da hannu wajen zubar da jini da manufofinsu na munafunci.”

KU KUMA KARANTA: Turkiyya za ta yi amfani da dukkan hanyoyin daƙile zalunci a Gaza – Shugaba Erdogan

Da yake ishara da mummunan harin da Isra’ila ta kai kan al’ummar Falasdinu da ke jiran agaji a unguwar Al Nabulsi da ke Zirin Gaza, Shugaba Erdogan ya ce, “Turkiyya tana matuƙar damuwa da wannan dabbanci na Isra’ila.”

Harin da aka kai ranar Alhamis yayin da ake kai agaji a arewacin Gaza ya kashe Falasdinawa 112.

Shugaban na Turkiyya ya ƙara da cewa, al’ummar duniya za su iya biyan bashin da suke bin al’ummar Falasdinu ne ta hanyar kafa kasar Falasdinu, inda ya sake nanata furucin Ankara kan wajabcin kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta da kuma saka Gabashin Kudus a matsayin babban birninta bisa sharuɗɗan 1967.

Taron diflomasiyya na Antalya ya karɓi baƙuncin wakilai daga kasashe 147, da mahalarta 4,500, wadanda suka hada da shugabannin kasashe 19 da ministoci 73 da wakilan kasa da kasa 57.

A ƙarƙashin babban jigon “Daukaka Diflomasiya A Yayin da ake fama da rikice-rikice”, taron ya yi nazari kan batutuwa daban-daban na duniya, da suka hada da rikicin yanayi da ƙaura da ƙaruwar ƙyamar Musulmai, yakin cinikayya, da kuma ƙirƙirarriyar basira.

Dandalin na bana ya ƙunshi bangarori sama da 50 tare da kuma baje kolin nune-nune daban-daban.

Mahalarta taron sun hada da jami’an diflomasiyya da ‘yan siyasa da ɗalibai da malamai, da wakilai daga kungiyoyin farar hula da ‘yan kasuwa.

Daga cikin fitattun nune-nunen da baje kolin “Karni na Turkiyya” ya bayyana irin gudunmawar hangen nesa da Turkiyya ta bayar ga fasaha da makamashi da tsaro da masana’antu.

Taron ya kuma gabatar da “MafHar ila yau taron zai haɗa da nuna shirin “Bulletproof Dreams: Gaza Children Painters Exhibition”, wato Nunin zanen Yara na Gaza, wanda Sashen Sadarwa na Fadar Shugaban Ƙasar Turkiyya ya shirya domin bayyana matsalolin jinƙai da yara ke fuskanta a Gaza.arki masu hana harsashi: nunin zanen yara na Gaza.”


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *