Ɗan takarar Gwamnan PDP a Abia ya rasu

0
473

Farfesa Ikonne ya kasance tsohon mataimakin shugaban jami’ar PDP a jihar Abia Uturu, wanda Allah Ya yiwa rasuwa a ranar Laraba 25/01/23.

A wani sakon da iyalan gidan sa suka fitar sun shaida cewa “cikin jimamani da alhinin ina sanar da rasuwar mahaifina, Farfesa Eleazar Uchenna Ikonne, wanda ya rasu a babban asibitin ƙasa na Abuja a yau, 25 ga Janairu, 2023 da ƙarfe 4 na safe bayan gajeriyar jinya.

KU KUMA KARANTA:Ɗan Majalisar da ya faɗi a taron Tinubu a Jos ya rasu

Yana murmurewa bayan ya yi jinya a Burtaniya amma ya sake dawowa kwanaki kaɗan da suka gabata, wanda ya kai ga kama bugun zuciya da yawa wanda yayi sanadiyar mutuwarsa.

Za a sanar da jama’a ƙarin cikakkun bayanai da shirye-shirye yi masa sutura bayan tattaunawa iyalinsa.

Leave a Reply