Ƙungiyar motocin dakon mai na Najeriya ta fara yajin aiki ‘kan tsadar rayuwa’

0
132

Direbobin tankokin dakon man fetur a Najeriya sun fara yajin aikin a ranar Litinin sakamakon ƙarin kuɗin da ake kashewa a wajen ayyuka, saboda faduwa warwas da darajar kuɗin Naira ya yi karo na biyu a cikin shekara guda da kuma yanayin hanyoyin ƙasar, in ji wani jami’in ƙungiyar.

Ƙungiyar masu tankokin dakon fetur ta Najeriya NARTO, wadda ta haɗa dubban masu motoci da direbobin da ke da alhakin rarraba man fetur a ƙasar, na neman ƙarin kuɗin jigilar kayayyaki daga masu sayar da man saboda tashin farashinsa.

Ƙasar da ta fi kowacce ƙarfin tattalin arziki a Afirka na fama da matsalar tsadar rayuwa, inda hauhawar farashin kayayyaki ta kai kusan kashi 30 cikin 100 a watan Janairu – mafi girma a kusan shekaru 30 da suka gabata, bayan da Shugaba Bola Tinubu ya kawo ƙarshen tallafin man fetur, wanda ya kasance mai farin jini amma mai tsadar gaske, a watan Mayun da ya gabata tare da ɗage takunkumin da aka sanya a kan cinikin kuɗaɗen waje.

KU KUMA KARANTA: Dillalan magani sun shiga yajin aiki a Kano

An fara samun dogwayen layukan man fetur a Legas, babban birnin kasuwancin Najeriya, yayin da tasirin yajin aikin ya fara ƙamari.

“Duk ƙoƙarin da ake na ganin an inganta farashin sufurin kayayyaki a ayyukanmu ya ci tura, don haka ba mu da wani zaɓi illa yajin aikin. Har yanzu muna kan tattaunawa,” kamar yadda Olawale Afolabi, babban sakataren NARTO ya shaida wa Reuters.

Najeriya, a ƙarƙashin tallafin da tsohuwar gwamnatin ke bayarwa, ta ninka kuɗin dakon kaya zuwa naira 20.46 a kowace lita a shekarar 2021 domin tallafawa isar da man da kuma kula da farashin bai-ɗaya a faɗin ƙasar.

Sai dai cire tallafin man fetur ya kawo ƙarshen wajabcin da yake kan gwamnati na biyan kuɗin dakon kaya, wanda ya taimaka wajen ci gaba da kasancewar farashin kayan masarufi na bai-ɗaya a faɗin jihohin Najeriya 36.

Bayan cire tallafin, masu sayar da man fetur suna ƙara komawa zuwa ƙarin masu samar da jigilar kayayyaki na zamani ko kafa nasu jiragen ruwan don yin gogayya da waɗanda ƙungiyar NARTO ke wakilta.

“Babu wani saɓani,” in ji Clement Isong, shugaban ƙungiyar manyan dillalan mai na cikin gida, Major Energy Marketers Association of Nigeria, yana kare kawo ƙarshen tallafin da kuma yadda ya yi sanadin buɗe kasuwar.

Leave a Reply