Ɗaruruwan matasa da dattawa na APC a Yobe sun amince KMT ya tsaya takarar Gwamna a 2027 (Hotuna)

0
285
Ɗaruruwan matasa da dattawa na APC a Yobe sun amince KMT ya tsaya takarar Gwamna a 2027

Ɗaruruwan matasa da dattawa na APC a Yobe sun amince KMT ya tsaya takarar Gwamna a 2027

Ɗaruruwan Matasa da Dattawa na jam’iyyar APC daga ƙananan hukumomi 17 da ke faɗin jihar Yobe, sun amince da Kashim Musa Tumsa (KMT) ya tsaya a matsayin ɗan takarar gwamna a 2027.

Matasa da Dattawa daga lunguna da saƙo na ƙananan hukumomi goma sha bakwai na jihar Yobe ne suka shirya wannan taro don nuna goyon baya ga Alhaji Kashim Musa Tumsa MFR (KMT).

KU KUMA KARANTA: KMT ya ba da tallafin Naira miliyan 1 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Gulani

Maƙasudin su na shirya taron shi ne a fito da murya ɗaya masu fafutukar neman tsayawa takarar Gwamna na Alhaji Kashim Musa Tumsa a zaɓen 2027 mai zuwa.

Sun haɗu ne a ƙarƙashin wani dandali mai suna “Zauren Matasa da Dattawan APC na Yobe”

Ko’odinetar kungiyar ta jiha Hauwa Idriss Kalallawa yayin da take jawabi a wajen taron, ta zayyana wasu karimci da Kashim MusaTumsa ya yi wa talakawa inda ta yi nuni da cewa hakan ne ya sa ƙungiyar ta yanke shawarar amincewa da shi a matsayin ɗan takarar gwamna a zaɓen 2027.

Sauran waɗanda suka gabatar da jawabai a yayin taron da suka haɗa da Darakta Janar na ƙungiyar Kashim Musa Tumsa, da sauran manyan masu ruwa da tsaki sun bayyana mutumin a matsayin mai tawali’u da kirki wanda ya cancanci zama gwamnan jihar Yobe mai zuwa 2027.

Taron ya samu halartar manyan mutane daga ƙananan hukumomin jihar 17.

Leave a Reply