No menu items!

Sample Page Title

Date:

Ba a san dalilin da ya sa ɗansandan ya hallaka kansa har lahira ba. Rahotanni daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno, sun bayyana cewar wani Sufeton ɗansanda ya hallaka kansa har lahira a jihar.

Marigayin na aiki ne da ofishin ’yansanda na Gwange a Borno. Wasu majiyoyi daga yankin, sun bayyana cewar ɗansandan na cikin ƙoshin lafiya kwanaki uku da suka wuce.

Ya zuwa yanzu dai ba a san dalilin da ya sa jami’in ya ɗauki wannan mummun mataki ba. Amma wani maƙwabcinsa da ke Layin Baya a unguwar Wulari Jerusalem a Maiduguri ne, ya ja hankalin mutanen yayin da ya ɗansandan ya ɗauki lokaci bai fito ba kuma wani wari na fitowa daga ɗakinsa.

Nan take aka kai rohoton faruwar lamarin hedikwatar rundunar ‘yansandan Borno, inda aka aike jami’ai zuwa wajen da lamarin ya faru.

KU KUMA KARANTA:Ƴan sandan Ghana sun ƙwato yarinya ƴar shekara 12 da ake zargi an yi wa aure

“A safiyar yau ne mutanen da ke gidan suka fara jin wani wari na fitowa daga ɗakinsa; kuma ƙofarsa a rufe ta ke ta baya. “’Yansanda sun zo kuma sun karya ƙofar ɗakin, inda suka iske gawarsa a kwance. A halin yanzu suna cikin gidan,” a cewar majiyar.

Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance da rundunar ’yan sandan jihar ta fitar game da faruwar lamarin.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...