Ƙasar Chadi ta sanar da ranar zaɓe don komawa tafarkin Dimokuraɗiyya

0
139

Hukumar zaɓen ƙasar Chadi ta ba da sanarwar ba zato a ranar Talata cewa, za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa wanda zai kawo ƙarshen mulkin soji na tsawon shekaru uku a yankin tsakiyar Afirka a ranar 6 ga watan Mayu.

Hukumar zaɓe ta ƙasar Chadi ta ce za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a ranar 6 ga watan Mayu. Ta ce zaɓukan za su dawo kan tsarin tafarkin mulkin dimokuraɗiyyar ƙasar, kuma za su kawo ƙarshen wa’adin mulkin Janar Mahamat Idriss Deby, wanda yanzu ya cika shekara ta uku.

Mahamat mai shekaru 37 ya zama shugaban kwamitin riƙon ƙwarya na sojojin Chadi a watan Afrilun 2021 bayan mutuwar mahaifinsa, Idriss Deby Itno, a lokacin da yake yaƙar ‘yan tawayen arewacin ƙasar. ‘Yan tawayen dai sun ce suna son kawo ƙarshen mulkin Deby na tsawon shekaru 31.

Shugaban ya karɓi mulki daga hannun mahaifinsa kuma ya yi alƙawarin jagorantar majalisar riƙon ƙwarya ta watanni 18, amma a watan Oktoban 2022 ya rusa majalisar tare da ayyana kansa a matsayin shugaban riƙon ƙwarya.

KU KUMA KARANTA:‘Yan hamayya a Chadi sun nemi Mahamat Idriss Deby ya janye daga tsayawa takara a zaɓen 2024

Har yanzu dai ba a san ko ‘yan takara nawa ne za su fafata a zaɓen na ranar 6 ga watan Mayu ba. Sai dai a watan da ya gabata, tsohuwar jam’iyyar Patriotic Salvation Movement ko MPS mai mulki a Chadi ta ce Mahamat Idriss Deby ne zai zama dan takarar jam’iyyar.

Wasu gungun ‘yan adawar ƙasar Chadi sun gana a ranar litinin, kwana guda gabannin bayyana ranar zaɓen, domin zaɓar dan takararsu. Su ma sun yanke shawarar marawa shugaba Deby baya.

Leave a Reply