‘Yan sanda sun kama mutum 2 da ake zargin sace mahaifiyar Rarara

0
148
Yan sanda sun kama mutum 2 da ake zargin sace mahaifiyar Rarara

‘Yan sanda sun kama mutum 2 da ake zargin sace mahaifiyar Rarara

Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta sanar da cafke wasu mutum biyu bisa zargin hannu a garkuwa da mahaifiyar fitaccen mawaƙin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara.

Mai magana da yawun rundunar a Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce “muna tsare da mutum biyu kan lamarin, muna ci gaba da bincike.”

Tun farko, Kwamishinan tsaro na Jihar Katsina, Nasiru Mu’azu ya ce an sace dattijuwar ce a daren Juma’a a ƙauyen Kahutu da ke Karamar Hukumar Ɗanja.

Mu’azu ya ce waɗanda suka sace matar sun yi hakan ta hanyar bi ta bayan gida, inda suka sace ta ba tare da jami’an da ke tsaron gidan sun sani ba.

Ya kuma bayyana cewa tuni aka tura jami’an tsaro waɗanda suka bazama cikin dazuka domin bin sawun ’yan bindigar.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar mawaƙi Rarara

Neptune Prime Hausa ta ruwaito shaidu a kauyen sun ce da misalin karfe daya na dare ne dandazon ’yan bindiga suka kutsa gidan dattijuwar suka yi awon gaba da ita.

“A kafa suka zo, ba su yi harbi ba a lokacin da suka ka yi awon gaba da ita cikin ’yan mintoci.

“Dattijuwar ba ta bijire musu ba a lokacin da suka memi ta biyo su.

“Duk da cewa ’yan bindigar sun samu wasu mutane a gidan, amma mahaifiyar Rarara kaɗai suka ɗauka.

“Babu wani yunƙuri da aka yi na tunkarar ’yan bindigar a lokacin da suke tafiya da ita saboda bindigogin da suke ɗauke da su,” in ji wani mazaunin ƙauyen na Kahutu.
Ya ce, “Watakila maharan sun bar baburansu ne daga nesa suka tako zuwa cikin ƙauyen a kafa.

“Muna rokon Allah Ya kuɓutar da ita cikin koshin lafiya domin tana taimaka mana sosai a wannan ƙauyen.

“Danta Rarara mai yawan taimakon al’umma ne, kuma ya kawo mana abubuwan ci gaba sosai a garinmu,” in ji shi.