No menu items!

Sample Page Title

Date:

An shiga firgici a safiyar Litinin kan rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da wani mawaƙin Juju ɗan Najeriya, Omoba De Jombo Beats tare da masu masa kiɗa a ranar Lahadi.

Rahotannin da ke yawo a yanar gizo na cewa, mawaƙin da ‘yan tawagarsa na dawowa daga wani taro lokacin da aka yi garkuwa da su. Legit Hausa ya wallafa.

Wani mawaƙi da aka fi sani da Boyebest, ya wallafa labarin a shafinsa na Instagram inda ya koka kan wannan lamari da ya faru a ƙarshen makon da ya gabata.

Boye Best ya yi wa labarin nasa taken, “An yi garkuwa da mawaƙi da dukkan tawagar makaɗansa, lallai Najeriya ta lalace.”

An gano cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba ne suka yi garkuwa da su bayan sun yi wani wasa a Abuja a ƙarshen mako, cewar Vanguard.

Boye Best ya ce:
“An yi garkuwa da Omoba De Jombo Beats da makaɗansa a hanyarsu ta zuwa Kogi daga Abuja bayan yin wasa a ranar Lahadi.

“Muna neman taimakon ku jama’a saboda masu garkuwan na neman naira miliyan 10 kudin fansa kan kowanne mutum ɗaya.”

A karshe Boye Best ya yi wa mawaƙin da masu masa kiɗa addu’ar fita daga hannun masu garkuwa da mutanen lami lafiya.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...