Yadda ta kasance a shari’ar ɗan China kan zargin kisan da ya yiwa Ummita

0
166

Babbar Kotun jihar Kano ta ɗage shari’ar Frank Geng Quangrong, ɗan ƙasar China da ake zargi da kashe budurwarsa ‘yar jihar Kano Ummukulsum Sani mai shekaru 22 a duniya.

Wanda ake tuhumar mazaunin yankin Railway a Kano, ana zargin sa da laifin kisan kai, sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin.

Mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar zuwa ranar 29 ga watan Maris, 2024 domin yanke hukunci.

Ya kuma ɗage zaman biyo bayan jawaban ƙarshe da lauyoyin masu gabatar da ƙara da masu kare ƙara, Muhammad Dan’azumi da Aisha Mahmoud suka yi.

Masu gabatar da ƙara sun rufe ƙarar da ke tuhumar dan China bayan gabatar da shaidu shida a ranar 21 ga watan Disamba, 2022.

KU KUMA KARANTA: An tsayar da ranar ci gaba da sauraron shari’ar ɗan China da Ummita

Haka kuma wanda ake ƙara ya gabatar da shaidu guda biyu da suka haɗa da likita, Dakta Abdullahi Abubakar.

A jawabinsa, wanda ake tuhumar ya shaida wa kotu cewa marigayiya Ummukulsum ta kai masa hari da wuƙa.

Lokacin da nake kare kaina, Ummukulsum ta cije ni a hannu da ɗan yatsana kuma ta yi min rauni a ‘ya’yan maraina na,” in ji Frank.

Ana zargin ɗan China da daɓa wa marigayiyar wuƙa a gidansu da ke unguwar Janbulo a Kano, a ranar 16 ga Satumban 2022.

Leave a Reply