Yadda masu sayen ƙuri’a suka kai wa jami’an EFCC hari a Kaduna

0
362

Jami’an hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziki tu’annati (EFCC) da ke aikin sa ido kan zaɓen Jihar Kaduna a yau, 18 ga Maris, 2023 sun fuskanci hari a titin makaranta, Unguwan Rimi Kaduna, a lokacin da suke yunƙurin kama wani da ake zargin mai sayen kuri’u ne.

Tawagar da ke aiki da bayanan sirri kan zargin wani Kabiru Musa da aka gani a cikin wani faifan bidiyo da ake zargin yana jawo masu kaɗa ƙuri’a ta hanyar amfani da wayarsa wajen tura kuɗi a asusunsu yayin da suke kaɗa kuri’a, sun haɗa kai don cafke wanda ake zargin.

Sai dai kuma nan take jami’an ‘yan sandan suka kama shi, sai Musa ya yi rashin gaskiya, ya yi kururuwa don jawo hankalin ‘yan ƙungiyarsa, inda suka yi ta kai farmaki kan jami’an, inda suka yi amfani da duk wani nau’in makaman da suka yi sanadiyyar jikkata wasu daga cikinsu jami’an.

KU KUMA KARANTA: Yadda aka kama wata mata ɗauke da kayan zaɓe na INEC a Legas

Jami’an sun yi namijin ƙoƙari inda suka yi biris da harin inda sun dage suka kama wanda ake zargin, kuma suka tafi da shi, inda wasu bata gari suka yi ta jifar da motarsu da duwatsu da wasu abubuwa masu haɗari waɗanda suka lalata gilashin motar sannan kuma jami’ai uku sun samu raunuka daban-daban.

Jami’an da suka jikkata a halin yanzu suna samun kulawar likitoci a cibiyar kula da lafiya ta shiyyar Kaduna, yayin da wanda ake zargin ke tsare, har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

Idan dai ba a manta ba an kai hari makamancin haka a lokacin zaɓukan shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar dokokin ƙasa, inda aka kai wa wasu motocinsu hari.

Da yake mayar da martani a kan lamarin, Shugaban Hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa ya yaba wa jami’an.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su daina kai wa jami’an hukumar hari domin ba za a amince da wannan mataki ba.

Leave a Reply