Yadda gobara ta ƙone shaguna 80 a Kano

0
350

Daga Saleh Inuwa, Kano

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce gobara ta ƙone shaguna 80 a kasuwar kurmi da ke ƙaramar hukumar Kano. Sanarwar ranar laraba a Kano ta bakin kakakin hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi, ta ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 05.23 na safe.

Abdullahi ya ce ma’aikatar ta samu ƙiran gaggawa daga wani Aliyu Alkasim cewa an samu tashin gobara a kasuwar. Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa kasuwar ta shahara wajen cinikin turare, ginger da fata.

Kakakin ya ce gobarar ta ƙone gaba ɗaya shaguna 6 na dindindin da kuma bude shaguna 74. Abdullahi, ya tabbatar da cewa ba a rasa rai ba kuma babu wanda ya jikkata.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Buni ya jajantawa gwamnati da jama’ar Borno kan gobarar kasuwa

Ya ce ana kan binciken musabbabin tashin gobarar. Abdullahi ya shawarci masu amfani da su da su kashe su kuma katse duk wani na’urorin wutar lantarki da kuma gujewa amfani da wuta tsirara, musamman a harabar kasuwa.

Leave a Reply