Wani hari ta sama da Isra’ila ta kai Rafah ya kashe mutane 9

0
639

Ƙasashen duniya sun yi ƙira ga Isra’ila da ta taƙaita ayyukanta a birnin Rafah da ke kan iyaka da kudancin ƙasar, inda miliyoyin ‘yan gudun hijira suka fake.

Wani hari ta sama da Isra’ila ta kai kan wani gida a birnin Gaza da ke kudancin ƙasar ya kashe aƙalla mutane 9, shida daga cikinsu yara ne, a cewar hukumomin asibitin yankin a ranar Asabar, wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kusan tsawon watanni bakwai a yankin na Falasɗinawa da ta yi wa ƙawanya.

Yaƙin da Isra’ila ke yi da ƙungiyar mayaƙan Hamas ya haddasa fargaba a yankin gabas ta tsakiya da ke fama da rikice-rikice.

KU KUMA KARANTA:Iran ta kai hari mafi muni kan Isra’ila

Harin da aka kai da yammacin ranar Juma’a ya shafi wani gini da ke yammacin yankin Tel Sultan a birnin Rafah, a cewar jami’an tsaron farin kaya na Gaza. An kai gawarwakin yaran shida, da mata biyu da namiji ɗaya zuwa asibitin Abu Yousef al-Najjar da ke Rafah, kamar yadda bayanan asibitin suka nuna.

A asibitin ‘yan uwan mamatan sun yi ta kuka tare da rungumar gawarwakin yaran, da aka naɗe da farin ƙyalle, yayin da wasu suka yi ta jajanta musu.

A yayin wani taron manema labarai ranar Juma’a, a wurin taron ƙungiyar ƙasashen G-7 da aka yi a ƙasar Italiya, Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya faɗi cewa gwamnatin Biden “ba za ta goyi bayan wani gagarumin farmakin soja a Rafah ba.”

Leave a Reply