Turkiyya ta musanta zargin da ake mata na alaƙa da Isra’ila

0
160

Turkiyya ta musanta zargin da ake yi mata na haɗa kai da Isra’ila musamman ta ɓangaren makamai, inda ƙasar ta ce ba za ta taɓa yin wani abu da zai cuci Falasɗinawa ba.

“Ba zai yiwu a ce Jamhuriyar Turkiyya da ke goyon bayan Falasɗinu a ko da yaushe ba ta iya aiwatarwa ko kuma yin duk wani aiki da zai cutar da Falasɗinawa,” kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar ta sanar a ranar Talata.

Ma’aikatar ta ce ba ta da wani haɗi da Isra’ila, “daga ciki har da atisayen soji da batun haɗin kai kan tsaro.”

Wannan sanarwar na zuwa ne bayan wasu labaran ƙarya da aka rinƙa yaɗawa a kafafen sada zumunta waɗanda ke cewa Turkiyya na ci gaba da kai garin harsashin bindiga da makamai zuwa Isra’ila.

KU KUMA KARANTA: Masana kimiyya na Turkiyya sun gano wata ƙwayar halitta da ke jawo ciwon ƙoda ga yara

A ɗayan ɓangaren kuma, Ma’aikatar Sadarwa ta Turkiyya ita ma ta yi watsi da wannan rahoton bayan ganin an wallafa labaran ƙarya irin waɗannan da dama.

“Kayayyakin da ke a lamba ta 93 a jerin kayayyakin da ake zargin ana fitarwa ba kayayyakin yaƙi bane, amma kayayyakin gyara ne da kayayyakin kamun kifi da mutane ke amfani da su wurin wasanni da farauta,” kamar yadda ta bayyana a shafin X.

Kamar yadda alƙaluma suka nuna daga Hukumar Ƙididdiga ta Turkiyya, ba a fitar da wasu bindigogi na wasanni da farauta ba tun daga Mayun 2023.

Leave a Reply