No menu items!

Sample Page Title

Date:

Majalisar Zartarwa ta amince da naira tiriliyan 27.5 a matsayin kasafin kuɗin Najeriya na shekarar 2024.

Dangane da hakan ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gabatar wa Majalisar Tarayya kasafin a ranar Laraba mai zuwa.

Sakataren bincike da yaɗa labarai a Majalisar Tarayya, Dokta Ali Barde Umoru ya tabbatar da haka a yammacin yau.

A ƙunshin kasafin da Majalisar Zartarwar ta amince da shi, an tsaida farashin gangar mai a kan $73.96 da lissafin cewa za a rika hako ganguna miliyan 1.78 a rana da kuma farashin duk dala guda a kan N750.

Wannan ne cikakken kasafi na farko da Bola Tinubu zai gabatar wa majalisar tun bayan rantsar da shi a watan Mayun da ya wuce.

KU KUMA KARANTA: Babu ɗalibin da zai bar makaranta saboda rashin kuɗi a mulkina – Tinubu

Gabatar da kasafin ya nuna cewa Mista Tinubu zai ci gaba da tafiyar da tsarin kasafin kuɗin daga Janairu zuwa Disamba kamar yadda tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...