Sojoji sun lakaɗa wa jami’an YOROTA duka a Yobe

0
464
Sojoji sun lakaɗa wa jami'an YOROTA duka a Yobe
Jami'an YOROTA

Sojoji sun lakaɗa wa jami’an YOROTA duka a Yobe

An kwantar da wani jami’in hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Yobe (YOROTA), Yunusa Mohammed, a asibiti bayan ya sha dukan-kawo-wuƙa da ake zargin sojojin Najeriya na bataliya ta 241 da ke Nguru a jihar Yobe.

Neptune Prime ta samu labarin cewa lamarin ya auku ne a ranar Litinin ɗin da ta gabata sakamakon rashin jituwar da aka samu tsakanin jami’an YOROTA da wani jami’in Soji da ba a tantance ba da aka ce Laftanar ne.

Jami’an kula da zirga-zirgar ababen hawa ne suka tare sojan domin gudanar da bincike akai-akai kan babur ɗinsa wanda hakan ya harzuƙa jami’an rundunar.

Hakan ne ya kai ga sojan ya mari jami’in na YOTORA ɗin.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Buni Ya Kaddamar Da Motoci 20 Ga Kamfanin Sufuri Na Jihar

Wani shaidar gani da ido (an sakaya sunansa) ya bayyana cewa, bayan ya mari jami’in kula da zirga-zirgar ababen hawa ɗin, jami’in sojan ya tattaro abokan aikinsa daga bariki, waɗanda suka zo da ayarin motoci guda biyu zuwa ofishin Nguru na YOROTA, inda suka far wa duk wani jami’in da suka gani a harabar ofishin, wanda har suka iya kaiwa ga Yunusa Mohammed da ke fama da mummunan raunuka, sakamakon dukan da sojojin suka masa.

Yanzu haka Yunusa yana kwance a Asibitin gwamnatin tarayya dake Nguru inda yanzu haka yake jinya.

Leave a Reply