Shugaba kamfanin Neptune prime, Hassan Gimba, ya taya Gwamna Buni murnar sake lashe zaɓe

1
379

Shugaban Kamfanin yaɗa labarai na Neptune Network Nigeria Limited, mawallafin jaridun Neptune Prime da Neptune Prime Hausa a yanar gizo, Dokta Hassan Gimba, ya taya Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe murnar sake cin zaɓen gwamna a karo na biyu.

Dokta Gimba, wanda ya kai ziyarar taya murna ga zaɓaɓɓen Gwamna a gidan gwamnati, a Damaturu, ya ce nasarar Buni ta cancanci yabo, kuma ya yaba wa al’ummar jihar Yobe kan yadda suka amince da shugabancin gwamnan.

Ya ce gwamnan ya samu nasarar cin zaɓen sa ne ta hanyar nuna kyakkyawan shugabanci domin ci gaban jihar Yobe da kuma jin daɗin al’ummar jihar, kuma ya yi ta ƙoƙarin ganin jihar ta kai ga gaci.

A ranar Lahadin da ta gabata ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Gwamnan Jihar Yobe kuma ɗan takarar Jam’iyyar APC Mai Mala Buni a matsayin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan Jihar Yobe da aka gudanar ranar Asabar.

Gwamna Buni ya samu ƙuri’u 371,113 inda ya doke abokin hamayyarsa Sheriff Abdullahi na jam’iyyar PDP wanda ya samu ƙuri’u 104,259, yayin da Garba Umar na jam’iyyar NNPP ya samu ƙuri’u 14,246.

1 COMMENT

Leave a Reply