Shin dagaske an tuɓe kakakin ‘yan sandan Katsina saboda zargin cin zarafin ‘yar jarida?

0
1103

Daga Ibrahim EL-TAFSEER

Ku biyo mu don ku ji cikakken bayani da hujjoji daga kowane ɓangare

A cikin makon da ya gabata ne, wata ‘yar jarida kuma ‘yar rajin kare haƙƙin mata da ƙananan yara, Ruƙayya Aliyu Jibiya. Tana aiki ne a gidan Talabijin na Tambarin Hausa TV. Ta yi wani bidiyo a shafinta na Tiktok, inda take bayyana irin yadda rundunar ‘yan sandan jihar Katsina suke nuna fuskokin yara mata waɗanda ake zarginsu da karuwanci. Ta bayyana cewa hakan ba daidai bane.

“Ko a cikin ‘constitution’ na Nijeriya ba a ce a nuna fuskar wanda ake zargi a gidan Talabijin ko jaridu ba, har sai kotu ta tabbatar da abin da ake zarginsa akai. A nuna fuskar mace a ce ta yi karuwanci, to mace tana zama karuwa ne ba tare da namiji ba. Shi me ya sa ba za a kamo shi a haɗa su a nuna fuskarsu tare da ba?. Idan aka nuna fuskar mace ana zarginta da karuwanci, sai kuma kotu ta wanke ta daga zargin, to yaya za a yi da ita, bayan an riga an nuna ta a matsayin karuwa. Babu wanda zai aure ta sai dai rayuwarta ta ƙare a karuwancin. Shikenan an riga an cuci rayuwarta. Hukumar ‘yan sandan Katsina daku nake gaskiya ku gyara, hakan ba daidai bane” wannan shi ne abin da Ruƙayya ta faɗa a cikin bidiyon.

Kwatsam! Bayan kwana biyu sai ta sake yin wani bidiyon inda ta bayyana yadda rundunar ‘yan sandan jihar Katsina suka kamata, suka ci zarafinta, don ta wallafa wannan bidiyon.

Ga abin da ta bayyana a lokacin arangamarta da ‘yan sandan “Ina kan hanya ina tafiya, sai ‘yan Sanda suka biyo ni da motoci guda huɗu, suka tare ni akan hanya, suka sha gabana. Suka fiddo ni daga mota, suka fasa min waya, Gambo Isah (Kakakin ‘yan sandan jihar Katsina) ya murɗe min hanuna, ya ƙwace wayata, ya farfasa min ita a ƙasa. Daga nan ya ɗauke ni, shi da sauran ‘yan Sanda, aƙalla mota 20 da wani abu, suka kai ni gidan Sarki. Bayan mun je wajen mai martaba, mai martaba yace a je a kai ni gidan yari, har sai ya neme ni”.

“Bayan mun je kotu, muka tarar Alƙali baya nan, saboda haka aka wuce da ni wajen ‘Area Commander’ bayan lauyoyi na sun shiga, sai aka ba da beli na, da nufin cewa in koma yau. Bayan na koma, Lauya na baya nan, area commander ya ce dole za a kai ni Hedikwata, domin Kwamishinan ‘yan Sanda yana nema na. Nasan abin da na fuskanta a wajen ‘yan Sanda, ban yarda na je Hedikwata ba. Saboda Lauya na baya nan. Na gudu, na ɓuya. Yanzu haka wannan magana da nake muku, na gudu, na ɓuya, saboda Lauya na baya nan, ban san me ‘yan sanda za su min ba idan naje. Akan maganar da na yi wadda ba ta da wani illa. Kuma ina da dama da zan yi ta. Amma kuma ga abin da ya haifar. Saboda haka na gudu na ɓuya, saboda rayuwata tana cikin haɗari”. Inji Ruƙayya.

Bayan bayyanar wannan bidiyo, sai jama’a suka yi caa akan batun, kowa yana tofa albarkacin bakinsa, ciki har da ‘yan jaridu, Lauyoyi da sauran jama’a. Ganin yadda ake ta ƙiraye-ƙirayen dole a bi mata haƙƙinta, kwatsam, sai gidan Talabijin na Tambarin Hausa TV, wanda ta bayyana anan take aiki, sai suka fitar da sanarwar wai ita ba ma’aikaciyarsu bace. Wannan sanarwa ta bawa jama’a da dama mamaki, musamman ‘yan jarida. Take ta wallafa katin shaidarta na dasu (I. D. Card) haɗe da takardar shaidar albashin da suke biyanta da kuma takardar shaidar ɗaukanta aiki a gidan Talabijin ɗin na Tambarin Hausa. Kuma abokan aikin ta na gidan Talabijin ɗin sun tabbatar da ma’aikaciyar Tambarin Hausa TV ce.

To bayyanar waɗannan takardun shaidar, shi ne ya sa gidan Talabijin ɗin suka ji kunya, suka cire waccar sanarwar cewa ita ba ma’aikaciyarsu bace. Sai suka sake fitar da wata, wai ita tsohuwar ma’aikaciyarsu ce. Wai ta yi aiki dasu ne a can baya. Amma kowa ya gane borin kunya suke yi. A lokacin da take tsananin buƙatar taimakonsu, a lokacin suka guje ta. Jama’a dai suna ta Allah-wadai da abin da gidan Talabijin na Tambarin Hausa TV suka yi wa Ruƙayya (wakiliyarsu ta jihar Katsina). Musamman ma ‘yan jarida.

Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah ya musanta abin da Ruƙayya ta faɗa, na cewa ‘yan sanda sun dake ta sun fasa mata waya. Sannan kuma yace rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ba sa nemanta kamar yadda ta faɗa. Amma kuma ya ce sun kai ta ƙara wajen mai martaba sarkin Katsina akan irin abubuwan da take yi na ɓatanci ga ‘yan sanda a shafin ta na Tiktok da Twitter.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, an cire kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina bayan da ya ci zarafin wata ‘yar jarida. Sai dai bayan bayyanar wannan rahoto, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya Adejobi Olumiywa, ya ce ba a cire Gambo Isa ba, ƙarin girma aka yi masa.

Ya ce ba a cire shi akan wani batun zargi ba, a’a hasalima an yi masa ƙarin girma ne, yanzu shi ke kula da jihohi biyu a matsayin kakakin ‘yan sanda na Katsina da Kaduna. Ba kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito ba.

Kuma shi kansa Gambo Isa ɗin ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, ya samu ƙarin girma. Ga abin ya faɗa cikin harshen turanci “Alhamdullillah. After 7yrs of excellent stewardship as PPRO Katsina Police command and with my subsequent elevation to the rank of CSP, the Inspector-General of Police, has ordered my posting as PPRO Zone 14, Katsina. I will be supervising the Public Relations units of Katsina and Kaduna states command. Alhamdullillah, Masha Allah”.

Wato “Alhamdullillah. Bayan shekaru 7 da na yi a matsayin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina (PPRO), yanzu kuma na samu ƙarin girma na samun muƙamin CSP. Babban sufeton ‘yan sanda ya ba da umarnin a ba ni muƙamin PPRO na Zone 14, Katsina. Zan kula da sashin hulɗa da jama’a na jihar Katsina da Kaduna. Alhamdulillah, Masha Allah”

Yanzu dai jama’a sun kasa kunne, sun zuba idanu, suna jira su ga yadda za a ƙarasa wannan shari’a tsakanin ‘yan sanda da ‘yar Ruƙayya Jibiya. Sannan Lauyoyi, ‘yan jarida daga ɓangarori daban-daban da ‘yan rajin kare haƙƙin ɗan’adam na Amnesty International duk sun shigo kan batun don tabbatar da an yiwa Ruƙayya adalci.

Leave a Reply