Sai An Ilimantar Da ‘Yan Jam’iyya Sosai Domin Sanin Hakkin Da Ya Rataya A Wuyan Su- Yariman Bakura

0
358

Daga; IMRANA ABDULLAHI.

SANATA Ahmad Sani Yarima ya bayyana cewa babban aikin da ke gaban kowa ce jam’iyya shi ne bayar da ingantaccen ilimin me ake nufi da siyasa da kuma matsayin yan jam’iyya a koda yaushe a cikin jam’iyyar.


Yariman Bakura, wanda yake tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Ahmad Sani Yarima ya bayyana hakan ne a cikin wani shirin gidan Talbijin na kasa NTA mai suna “Tuesday Live” a ranar Talata.

Ya kara da cewa, mafi yawan lokuta za a ga yayan jam’iyya ba su iya biyan kudin da ya dace su biya na kasancewarsu Ya’yan jam’iyyar sai lokacin da mutum ke son tsayawa takara kawai sannan ya hada dukkan kudin karo karo na jam’iyya ya biya lokaci guda domin kawai ya na son tsayawa takara.

Yarima ya ci gaba da cewa ” ya na da kyau Ya’yan jam’iyya su san irin hakkin da ke kansu na taimakawa jam’iyyar da suke ciki domin gujewa matsalar bayar da makudan kudi idan ana son Ya’yan Jam’iyyar su zabi wani ko wasu yan takarar da za su tsaya neman zabe su zama wakilai ko shugabantar al’ummar kasa”.

Binciken da wakilin mu ya gudanar ya nuna cewa a can shekarun baya da suka gabata, Ya’yan jam’iyya ne ke tafiyar da lamuran jam’iyyarsu ta hanyar biyan kudin ka’ida kamar yadda yake a kunshe a kundin tsarin jam’iyya musamman a lokacin PRP da dai sauransu.

Amma a yanzu lamari ya canza saboda dan takara ne ke sayen masu zaben fitar da dan takarar jam’iyya da makudan kudi da nufin ya tsayawa jam’iyyarsu takara.

Leave a Reply