Potiskum ta wakilci Yobe a gasar wasanni na ‘yan ƙasa da shekaru 13 na Arewa Maso Gabas

0
281
Potiskum ta wakilci Yobe a gasar wasanni na 'yan ƙasa da shekaru 13 na Arewa Maso Gabas

Potiskum ta wakilci Yobe a gasar wasanni na ‘yan ƙasa da shekaru 13 na Arewa Maso Gabas

Potiskum ta wakilci jihar Yobe a gasar ‘yan ƙasa da shekaru 13 na Arewa Maso Gabas (North East) na ‘yan makarantun Firamare wanda ake kira da Inter-primary school games competition, wanda Zonal UBEC ke ɗaukar nauyi.

Shi dai irin wannan wasanni ana farawa ne a matakin yankuna (zones) a jihohi. Kamar a jihar Yobe akwai zones guda uku, Zone A, Zone B da Zone C. Ana buga wasa a tsakanin ƙananan hukumomin yankin, har a fitar da wanda ya yi nasara a tsakaninsu.

Idrissa Dahiru shi ne Chief Coach na makarantun Firamare a ƙaramar hukumar Potiskum, a tattaunawarsa da Neptune Prime ya bayyana yadda ya yi nasara har ya wakilci jihar Yobe a gasar wasanni ta Arewa Maso Gabas, da shi da yaransa.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Abba ya canza sunan cibiyar horas da wasanni zuwa sunayen ‘yan wasan Kano 22 da suka mutu

Idrissa ya fara ne da cewa “Tun da farko sai da muka yi wasa a tsakanin ƙananan hukumomin yankin Zone B. Wato Potiskum, Fika, Fune da Nangere, inda Potiskum ta doke su duka. To wannan ne ya bawa Potiskum dama ta tafi buga wasa a matakin jiha. Wato za a buga wasa a tsakanin waɗanda suka yi nasara a kowane yanki (zones).

An buga wasa tsakanin Damaturu da Yusufari, inda Yusufari ta doke Damaturu. Sai aka buga wasa tsakanin Potiskum da Gulani, inda Potiskum ta doke Gulani. Sai aka buga wasan ƙarshe tsakanin Potiskum da Yusufari, inda Potiskum ɗin ta doke Yusufari. Wannan shi ne ya bawa Potiskum damar wakiltar jihar Yobe a gasar wasanni na ‘yan ƙasa da shekaru 13 na Arewa Maso Gabas (Inter-primary school games competition) Adamawa 2025.

Ya ci gaba da cewa “bayan mun isa Adamawa, sai muka shiga tantancewa (screening). To a tantancewar sun cire min ‘yan wasa 6, wai shekarunsu ya haura 13. Don haka sai na ɗauko yara guda 6 daga cikin ‘yan wasan volleyball da Handball da na tafi da su, sai na maye gurbin waɗannan yara 6 da aka cire min.

Wasanmu na farko an haɗa mu da jihar Borno, inda muka doke Borno da ci 3 – 0 da babu. Wasanmu na biyu da Bauchi ne. Bauchi sun zo da ‘yan wasan da shekarunsu ya haura 13. Don haka sai kawai aka ba mu nasara akansu. Wasanmu na 3 da Gombe ne. Gombe sun yi nasara a kanmu da ci 4 – 1. Sai aka buga wasan ƙarshe tsakanin Gombe da Adamawa.

Yobe ita ce ta zo na uku a gasar (third position). Sai dai daga ‘yan wasan Yobe an samu best player. An ba mu medals da Certificate. Sannan an zaɓi ‘yan wasan Yobe 2 za su buga wasa a matakin ƙasa gaba ɗaya.

Muna godiya a Gwamnan Yobe Dakta Mai Mala Buni da shugaban ƙaramar hukumar Potiskum, Alhaji Salisu Mukhtari da SUBEB da kuma Education Secretary.

Leave a Reply