Gwamna Abba ya canza sunan cibiyar horas da wasanni zuwa sunayen ‘yan wasan Kano 22 da suka mutu
Daga Jameel Lawan Yakasai
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya girmama sunayen ‘yan wasa 22 da suka rasu a wani mummunan hatsari a hanyarsu ta dawowa Kano daga Gasar Wasannin Kasa da aka gudanar a watan Mayu 2025, ta hanyar sanya sunayensu a tarihi.
Gwamna Abba Kabir ya bayyana cewa, waɗannan ‘yan wasa sun sanya Jihar Kano alfahari, don haka ya dace a ci gaba da tunawa da su har abada.
A wata sanarwa da Babban Sakataren yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano, Mustapha Muhammad, ya fitar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa daga yanzu, cibiyar wasanni ta jihar Kano za a dinga kiranta da sunan “Cibiyar Wasanni ta ‘Yan Wasa 22 na Jihar Kano.”
Sanarwar ta ƙara da cewa, Hukumar Wasanni ta Jihar Kano za a sake mata suna zuwa “Hukumar Wasanni ta ‘Yan Wasa 22 na Jihar Kano.”
KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano ta ba da umarnin farfaɗo da makarantar Faransanci da Sinanci a jihar
Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana wannan batu ne yayin wata ziyarar ban girma da tawagar Mai Dakin Shugaban Ƙasa, Hajiya Remi Bola Ahmed Tinubu, ta kai masa, inda ta bayar da gudummawar Naira miliyan ɗari da goma sha ɗaya (₦110,000,000) ga iyalan ‘yan wasan 22 da suka rasa rayukansu a mummunan hatsarin da ya faru kilomita biyar kacal kafin su isa Kano.
Gwamnan ya ce waɗannan ‘yan wasa jarumai ne da suka fafata domin ganin Kano ta yi fice a Gasar Wasannin Kasa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta dauki nauyin karatun ‘ya’yan ‘yan wasan da suka mutu, sannan za a sanya matansu cikin shirye-shiryen tallafin gwamnati.
Haka kuma, ga waɗanda ba su da mata, gwamnati za ta kula da iyayensu ta hanyar haɗa su cikin shirye-shiryen tallafi da bunƙasa rayuwa.