Ana fargabar mutane da dama sun rasa rayukansu bayan da wata tankar mai ta kama da wuta a hanyar East-West Road a birnin Fatakwal da ke jihar Rivers a kudancin Najeriya.
Jaridun Punch da na Vanguard sun ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:45 na daren Juma’a.
Bayanai sun yi nuni da cewa bayan da tankar ta mai ta kama da wuta, ta shafi motoci aƙalla goma da ke jerin cunkoson ababen hawa a birnin na Fatakwal.
KU KUMA KARANTA:Matatar man Fatakwal za ta koma bakin aiki cikin watan Afrilu – Kyari
Wani da ya shaida lamarin ya faɗawa jaridar Vanguard cewa ya ji ƙara har sau biyu masu firgitarwa daga baya kuma hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniya.
“Idan kuna da ‘yan’uwa a Fatakwal ku ƙira su don ku ji lafiyarsu” Wani mazaunin birnin na Fatakwal mai suna Bassey Esang Don, ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba a san musabbabin fashewar da ta auku ba ko iya sanin adadin mutanen da suka mutu.
Faɗuwar tankar mai ta kama da wuta ba baƙon abu ba ne a Najeriya, inda a wasu lokuta mutane kan yi rububin zuwa kwasar man idan yana Malala.
Daga nan ne kuma akan samu akasi har wuta ta kama ta laƙume rayukan mutane.
Wannan al’amari na faruwa ne yayin da farashin mai ya ƙara tsada a Najeriya inda litar mai ta kusa kai wa Naira 1,000 a sassan ƙasar.