Mutane 2 sun mutu, 2 sun jikkata, sakamakon rikici a kan iyakar gona a Yobe

0
185
Mutane 2 sun mutu, 2 sun jikkata, sakamakon rikici a kan iyakar gona a Yobe

Mutane 2 sun mutu, 2 sun jikkata, sakamakon rikici a kan iyakar gona a Yobe

Rundunar ‘yansandan jihar Yobe, ta yi Allah-wadai da rikicin da ya ɓarke wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyu tare da jikkata wasu biyu a ƙaramar hukumar Gulani.

A cewar rahotannin ‘yansanda, lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 9 ga watan Agusta, 2025, da misalin karfe 11:30 na safe, bayan wani mummunan hari da aka kai kan rikicin gonaki tsakanin mazauna garin Zango (ƙaramar hukumar Gulani) da kuma Azare da ke (ƙaramar hukumar Gujba). Ƙauyukan biyu suna kan iyaka ne tsakanin ƙananan hukumomin biyu.

KU KUMA KARANTA: An kashe mutum 1, da dama sun jikkata a rikicin manoma da makiyaya a Yobe

Waɗanda harin ya rutsa da su Sani Maƙeri mai shekaru 40 da Abdullahi Maicitta mai shekaru 35 dukkansu mazauna garin Zango sun rasa rayukansu a harin, yayin da wasu biyu suka samu munanan raunuka. Ba tare da ɓata lokaci ba aka kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibitin ƙwararru dake Damaturu domin duba lafiyarsu.

Rundunar ‘yansandan ta mayar da martani cikin gaggawa bayan da Hakimin Ƙauyen Zango ya yi masa kira shi a waya kan lamarin, kuma tuni suka fara farautar waɗanda suka aikata wannan aika-aika, inda suka arce daga wurin.

A cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yansandan, SP Dungus Abdulkarim, rikicin gonakin ya ta’azzara ne tun lokacin noman da ya wuce. Duk da yunƙurin da ‘yansanda da kwamitin daidaita iyakokin jihar suka yi a baya, ana ci gaba da samun takun saƙa tsakanin al’ummomin biyu.

KU KUMA KARANTA: ‘Yansanda a Yobe sun kama wani matashi bisa zargin kisan kai

Kwamishinan ‘yansanda, CP Emmanuel Ado, psc, fdc, ya yi kakkausar suka ga harin tare da jaddada aniyar rundunar na gurfanar da waɗanda ke da hannu a gaban kuliya. “Rundunar ‘yansandan jihar Yobe ba za ta amince da duk wani nau’i na rashin bin doka da oda ba, ko kuma ramuwar gayya ba, duk mutanen da aka samu da laifi za su fuskanci cikakken hukuncin doka,” inji shi.

Rundunar ‘yansandan ta kuma shawarci manoma da sauran al’umma da su mutunta kan iyakokin da aka kafa da kuma bayar da rahoto ta hanyar doka da lumana.

Rundunar ‘yansandan ta ce za a gurfanar da dukkan ɓangarorin biyu da abin ya shafa a gaban kotu domin tabbatar da adalci ga waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata, tare da hana ɓarkewar rikicin nan gaba.

Leave a Reply