An kashe mutum 1, da dama sun jikkata a rikicin manoma da makiyaya a Yobe
Daga Ibraheem El-Tafseer
Wani rikici da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a ƙauyen Chukuriwa da ke ƙaramar Hukumar Nangere a Jihar Yobe, ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu da dama.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, 13 ga watan Mayu, 2025 bayan da wani makiyayi ya shigar da shanunsa cikin gonar wani manomi, inda hakan ya tayar da rikici.
A lokacin da rigimar ta ɓarke, an harbi wani manomi mai suna Babayo Maina Osi da kibiya a goshinsa, wanda hakan ya jikkata shi.
KU KUMA KARANTA:Gwamna Yobe ya ziyarci sansanin soji da ke Buni Gari, ya tallafawa iyalan Sojojin da aka kashe
Wata majiya daga ƙauyen ta ce rikicin ya ƙazanta sosai har ya rikiɗe zuwa faɗa tsakanin manoma da makiyaya.
A lokacin wannan faɗa ne aka harbi wani mutum mai suna Usman Mohammed, mai shekara 35 da kibiya, wanda daga bisani ya rasu a Babban Asibitin Nangere.
Jami’an tsaro sun isa wajen domin daƙile rikicin da kuma hana rincaɓewa rikicin.
Rahoton ya bayyana cewa an ƙwato shanu biyu, awaki 29 da raguna daga hannun manoman da ake zargi sun ƙwace daga hannun makiyaya.
A yanzu haka, an gayyaci shugabannin ɓangarorin biyu domin tattaunawa da kuma tabbatar da cewa irin wannan rikici bai sake faruwa ba a nan gaba.
Duk ƙoƙarin da Neptune Prime ta yi don jin ta bakin kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkareem, ya ci tura, domin bai ɗaga waya ba.