Muna roƙon gwamnati ta taimaka a sake mu – Amarya da ‘yan biki da aka sace suna roƙo (Bidiyo)

0
200

Daga Ibraheem El-Tafseer

A wani faifayin bidiyo da ‘yan bindigar masu garkuwa da mutane suka fitar, sun nuna Amarya da sauran ‘yan bikin su 63 da suka yi garkuwa da su. ‘Yan bindigar sun bayyana cewa gwamnati ta daina ƙarya na rage adadin waɗanda suka kama, amarya da ‘yan biki 63 suka kama suke a hannun su yanzu haka, ba 35 kamar yadda gwamnati take ta sanarwa ba. Kuma har yanzu suna hannunsu.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun sace mahalarta ɗaurin aure 35 a Najeriya

A bidiyon shugaban masu garkuwa da mutanen ya bayyana cewa “waɗannan da kuke gani ni ne nake riƙe da su, idan ba a biya wannan kuɗi ba, Naira miliyan 100, to ba za mu sake su ba. Idan kuma akwai wanda zai iya ƙwace su, to ya zo ya gwada. Amarya kuma idan ba a zo an fansheta ba, za mu ɗaura mata aure da wani” inji shi

A cikin bidiyon an nuno Amarya da sauran ‘yan bikin su 63, suna roƙon gwamnati da ta taimaka ta karɓo su, suna faɗin “a taimaka a biya kuɗin fansar, a sake mu, mu dawo gida. Ba su cutar da mu ba ko kaɗan, tun da suka tafi da mu” inji su.

Kalli bidiyon a nan:

Leave a Reply