Muna Biyayya Ga Gwamna Ganduje Da Uwar-Gidansa – Inji Hajiya Alpha Dambatta

0
374

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

WATA Jigo a jam’iyyar APC daga Karamar hukumar Dambatta wadda Kuma aka fi sani da “Maman Maja” watau Hajiya Alpha Abdul Usman Dambatta, ta ce suna nan tare da gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje da kuma mai dakinsa a tafiya irin ta siyasa domin ci gaban Jihar Kano.

A cikin wani shiri da wata kafar labarai ta yi da ita, Hajiya Alpha Abdu Usman Dambatta wadda Kuma har ila yau ake Yi Mata kirAri da Uwar marayu, ta bayyana cewa a siyasar wannan zamani, gwamnatin Jihar Kano bisa jagorancin Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta yi kokari kwarai da gaske wajen tabbatar da cewa al’ummar Jihar Kano suna rabauta da ribar dimokuradiyya ba tare da nuna gajiyawa ba tun daga shekara ta 2015.

Sannan ta nunar da cewa al’ummar Jihar Kano sun yarda cewa gwamnatin Ganduje ta yi kokari sosai wajen bunkasa Jihar ta fannoni daban-daban duk da irin kalubalen da aka rika cin karo dasu kamar yadda tsarin dimokuradiyya ya gada tun da kasarnan ta koma kan tsarin mulkin siyasa a shekara ta 1999.

Haka kuma Maman Maja, Hajiya Alpha Dambatta ta bayyana mai dakin Gwamnan, Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje a matsayin uwa tagari wadda kuma take da kishin al’ummar Jihar Kano musamman mata da matasa da Kuma yara kananana da suke da matukar bukatar tallafi.

Ta yi amfani da wannan dama inda ta godewa Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje da Uwargidansa Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje saboda kokarin da suke yi wajen ganin suna kyautata zamantakewar al’ummar jihar Kano ta kowane fanni ba tare da nuna gajiyawa ba, wanda a cewar ta jihar kano ta zamo abar misali cikin Jihohin wannan kasa.

Dangane da abubuwan da suke faruwa na rikicin cikin gida a jam’iyyar APC a kano kuwa, Hajiya Alpha Dambatta ta ce wannan ado ne a dimokuradiyya, amma gwamna da dukkanin masu ruwa da tsaki suna kokarin kawo daidaito a tafiyar da siyasar jihar duba da yadda yanzu an dauki matakai na kara karfin jam’iyyar musamman wajen fitar da Yan takara a dukkanin matakai da za a fafata dasu a zaben 2023.

A karshe, Hajiya Alpha Abdu Usman Dambatta, uwar marayu, ta yi fatan ci gaba da samun dawamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Kano da Kuma kasa baki daya ta yadda zabukan da za a gudanar zasu zamo masu albarka ga al’ummar kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here