Mazauna yankunan Minjibir a Kano sun koka kan lalacewar hanya

0
195
Mazauna yankunan Minjibir a Kano sun koka kan lalacewar hanya

Mazauna yankunan Minjibir a Kano sun koka kan lalacewar hanya

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Al’ummar karamar hukumar Minjibir sun koka kan yadda hanyar su daga Ungoggo zuwa Minjibir ta zama tarkon Mutuwa, sakamakon lalacewar data yi , tun bayan da aka yi mata kimanin shekaru 40 da suka gabata.

Mutanen sunce hanyar a yanzu haka tana cin rayukan mutane sakamakon ramukan dake kanta, a yayin da duk lokacin da aka yi ruwan sama, babu halin bi ta hanyar.

KU KUMA KARANTA: Mum shafe kwanaki 40 babu wutar lantarki – Mazauna lokon Maƙera ta jihar Kano

Daya daga cikin mutanen Minjibir, mai suna, Muhammad Nata’ala Umar, ya ce gwamnatocin baya sunsha yi masu alkawarin gyara hanyar, ta Ungoggo zuwa Minjibir amma har yanzu ba’a yi masu gyaran ba, duk da koken da suka jima suna yi.

To sai dai a martanin da shugaban karamar hukumar Minjibir Kaftin Jibrin Nalado, a yanzu haka suna kan dakon ganin anzo ayi gyaran hanyar, kasancewar a kwanakin baya an turo jami’ai daga ma’aikatar aiyuka da gidaje ta jihar kano domin duba yadda za a yi aikin hanyar.

Leave a Reply