NBS ta fitar da jihohin Najeriya uku da Rayuwa tafi Tsada da uku Kuma da Rayuwa tafi Sauki
Daga Shafaatu Dauda Kano
Hukumar kididdiga ta Najeriya NBS ta bayyana jihohin Enugu,Kebbi, da Neja a matsayin jihohin da suka fi tsadar rayuwa a Najeriya.
Hukumar ta bayyana hakan a cikin kididdigar yanayin tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki da ta fitar a watan Afrilun Shekarar 2025.
KU KUMA KARANTA:An samu raguwar hauhawar Farashi da kaso 23.71 a Najeriya – NBS
A cewar hukumar Jihar Enugu ce ke kan gaba wajen hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa a duk shekara, wanda ya kai kaso 35.98 cikin 100 , sai Kebbi da kaso 35.13 cikin 100, sai kuma Naija mai kashi 34.85.
Wannan ya nuna cewa jihohin ukun sun sami hauhawar farashin kayayyaki mafi girma a Najeriya.
A gefe guda kuma hukumar ta NBS ta fitar da jihohi uku da rayuwa tafi sauki a duk Najeriya da suka hada da , jihar Ondo, ta dauki kaso 13.42 cikin 100 da Cross River, da kashi 17.11 cikin 100; da Kwara, da kashi 17.28 cikin 100.
Wannan na zuwa ne bayanda farashin kayayyaki a Najeriya ya ragu zuwa kashi 23.7 cikin 100 a cikin watan Afrilu.
Neptune prime Hausa ta rawaito cewa a watan Mayun 2024, NBS ta bayyana jihohin Kogi, Bauchi da Oyo a matsayin jihohin da sukafi tsadar rayuwa.