Boko shirme ne, ku koyi aikin tela da tuƙu, inji Gwamnan Bauchi
A wani Faifayin bidiyo da ke yawo a social media ya jayo ce cece-kuce, inda aka nuno Gwamnan Bauchi Bala Abdulƙadir Muhammad ya ke cewa ai karatun Boko ba dole bane.
Ya ce “Ku gyara kanku ku daina shaye-shaye, ku daina abubuwan da zai gushe muku da hankali, karatu ba sai ka je ka yi Boko ba. Ni Bala ban yi Boko ba amma kun ga Bala ya zama Bala.
KU KUMA KARANTA: Ba za mu sauya tsarinmu na rufe makarantu a watan Azumi ba – Gwamnonin Kano, Bauchi, da Kebbi
Ku gyara halayenku karatun Boko duk shirme ne, amma idan kana da karatun Muhammadiyya to ka mallaki hankalinka, ka san abin da ka ke so ka yi ko wajen noma ko sana’a shi ne karatun fa, kuma ya ce duk wani babban mai arziƙi da direba (tuƙi) ya fara ko kuma Tela, kar a raina sana’a.