Mambobin ASUU su kwantar da hankalin su kan batun albashi – Gbajabiamil

Kakakin majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamil, ya umarci mambobin ƙungiyar ASUU da su kwantar da hankulansu game da iƙirarin da malaman suka yi na cewa an biya su rabin albashin watan Oktoba.

A wata sanarwa da ya sanya wa hannu, kakakin majalisar wakilan ya ce suna aiki domin magance wannan matsala da ta sake tasowa.Ya ƙara da cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na son a duba wannan batu, domin magance shi.

“A lokacin da ASUU ta janye yajin aikinta mako uku da suka gabata, mun yi zaton cewa dalibai za su koma makarantu domin ci gaba da karatu a jami’o’in kasar”, in ji Gbajabiamila.

Ya ce Majalisa da ɓangaren zartarwa za su yi aiki tare domin magance matsalolin da suka haddasa yajin aikin, yana mai cewa yanzu haka majalisar na aiki a kan ƙudurin kasafin kuɗin 2023, wanda ya tanadar wa ƙungiyar kuɗaɗen da suke buƙata domin raya jami’o’in kasar.


Comments

3 responses to “Mambobin ASUU su kwantar da hankalin su kan batun albashi – Gbajabiamil”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Mambobin ASUU su kwantar da hankalin su kan batun albashi – Gbajabiamila […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Mambobin ASUU su kwantar da hankalin su kan batun albashi – Gbajabiamila […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *