Daga Maryam Umar Abdullahi
Hukumar Alhazai ta ƙasar Ghana ta sanar da shirye-shiryen ta na aikin hajjin bana a ƙasar Saudiyya. A yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a masauƙar alhazai da ke Accra, shugaban hukumar Alhaji Ben Abdallah Banda ya sanar da kuɗin hajjin bana a hukumance.
Alhaji Banda, yace duk da ƙarin kuɗaɗe da aka samu na gudanar da aikin Hajji a ƙasar Saudiyya a bana, hukumar alhazan Ghana, bayan ta yi nazari sosai, tace za ta cika alƙawarin da ta ɗauka na ƙin ƙarin kuɗin hajjin bana.
Alhaji Banda ya ce, har yanzu kuɗin hajjin bana bai sauya ba, maniyyata za su biya GHC 75,000, wanda ya yi daidai da dalar amurka $6,250.
“Mun yi alƙawari cewa, idan darajar dala ($) ta hau, kuma darajar sidi (GHC) ta sauko, ba za mu ƙara kuɗin hajjin wannan shekarar ba. Don mu cika alƙawarinmu, kuɗin hajji na wannan shekarar shi ne GHC 75,000. Don haka duk wanda yake da niyyar zuwa hajji wannan shekarar sai su fara biya yanzu ga ajentocin hukumar alhazai, ko a biya kai tsaye ga hukumar, ko kan manhajar da hukumar ta buɗe domin biyan kuɗin hajji daga ko’ina”, in ji shi.
Alhaji Banda ya ƙara da cewa, kuɗin na ƙunshe ne da farashin biza, kuɗin jirgi daga Ghana zuwa Saudiyya da dawowa; da sufuri daga Madina zuwa Makkah, Makkah zuwa Mashaa’ir, Mina, da Arafat, da Mashaa’ir zuwa filin jirgin saman Jiddah, da kuɗin otel, da ciyarwa a can na wata ɗaya da sauransu. Yace, za a rufe amsar kuɗaɗen maniyyata daga ranar 15 ga watar Maris 2024.
Babban Sakataren Hukumar, Alhaji Farouk Hamza, ya yi ƙira ga maniyyata da ka da su biya kuɗaɗensu ga wasu ajentocin da hukumar ba ta amince da su ba
KU KUMA KARANTA: Kotun Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce dole Isra’ila ta kaucewa kisan kiyashi a Gaza
“Kowa ya san bizan shekara ɗaya daban ne da bizan hajji. A nan Ghana, hukumar alhazai ce kaɗai gwamnatin Ghana da na Saudiyya suka amince da su gudanar da aikin zuwa hajji. Don haka, duk wanda yake da niyyar zuwa hajji, bai yiwuwa sai da hannun hukumar alhazai na Ghana”, a cewarsa.
Shugaban Ajentocin Hajji na Ghana, Alhaji Alhassan ya jaddada muhimmancin ƙin biyan kuɗaɗe ga ajen da hukumar ba ta aminta da su ba. Yace, shekarar da ta gabata sun bayyana matakin da za su bi wajen daƙile hakan, wanda ya yi sanadiyar rashin nasara, amma wannan shekarar ba za su bayyana ba.
Ya ƙara da cewa amma sun shirya tare da hukumar Saudiyya matakan da za su ɗauka na hukunta duk wanda aka kama.
Hukumar tace kamar shekarar da ta gabata, otel ɗin Ghana na kusa da masallaci ne a Madina, kuma a Makka, akwai bas-bas da za su yi jigilar alhazai zuwa harami kyauta.