Kungiyar AWIFCA Tana Kokari Wajen Kyautata Muhalli

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

BABU shakka, Kungiyar nan mai rajin kare muhalli da kyautata yanayin sa watau ” Arewa Women Initiative For Clinate Change Advocacy And Environmental Sustainability” (AWIFCA)” tana kokari wajen gudanar da muhimman aiyuka masu kyau dangane da batun kare muhalli.

Akwai manya da kananan kungiyoyi da ake dasu wadanda kuma suke kokari sosai wajen aiwatar da muhimman abubuwa na kyautatuwar zamantakewar al’umma wanda ko shakka babu Kungiyar (AWIFCA) tana daya daga cikin wadannan kungiyoyi kuma kwalliya tana biyan kudin sabulu wajen yiwa al’umma hidima ta fannoni daban-daban.

An kafa Kungiyar ta (AWIFCA) a shekara ta 2020, kuma bisa jagorancin shugaba Hajiya Alawiyya Baba Musa da sauran mata masu kishin kasa inda suka mayar da hankali kan harkar muhalli da samar da sahihan hanyoyi na magance dumamar yanayi wanda ko shakka babu ana samun ci gaba ingantacce ta fuskar kula da muhalli da kyautata yanayin zamantakewa a birni da yankunan karkara.

AWIFCA ta gudanar da wasu aikace-aikace wadanda Kuma suke da matukar muhimmancin gaske ga rayuwar dan adam wadanda kuma ba za a iya mantawa da su ba duba da yadda zamantakewar al’umma take da bukatar samun yanayi mai gamsarwa, inda kungiyar ta gudanar da dashen itatuwa a makarantu da ma’aikatu domin inganta muhalli da kuma yin abubuwa a fannin lafiya da samar da ruwan sha mai tsafta a wasu gurare zababbu.

Bisa yadda kafar sadarwa ta “Media Action-Nigeria” ta gudanar da bincike kan kungiyar (AWIFCA), ana samun nasarori wajen kyautata rayuwar al’umma tare da yin aiki da gaskiya wajen ganin al’umma suna rabauta daga manufofin kafa kungiyar kamar yadda ake gani a dukkanin inda Kungiyar ta sanya kafa.

Shugabar Kungiyar Hajiya Alawiyya Baba Musa ta jaddada cewa “zamu ci gaba da assasa dukkanin wasu abubuwa da zasu taimaki rayuwar al’umma musamman wadanda suka shafi muhalli da kula da lafiya da kuma fito da karin hanyoyi na magance afkuwar dumamar yanayi ba tare da nuna gajiyawa ba”.

Bisa ga yadda kungiyar ta (AWIFCA) ke Kokari a tsakanin al’umma, akwai bukatar ganin cewa ana baiwa kungiyar kulawa ta musamman daga gwamnatoci da mutane masu iko da kungiyoyi manya domin ganin an fadada aiyuka da kyautata rayuwar al’umma musamman ganin cewa aiyukan kungiyoyi yana bukatar tallafi daga ko’ina.


Comments

One response to “Kungiyar AWIFCA Tana Kokari Wajen Kyautata Muhalli”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Kungiyar AWIFCA Tana Kokari Wajen Kyautata Muhalli […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *