Kotun ICJ ta umarci Isra’ila da ta ɗauki matakan magance yunwar da ake fama da ita a Gaza

0
157

Alkalai a kotun ƙasa da ƙasa baki ɗayansu sun bai wa Isra’ila umarnin daukar dukkanin matakan da suka dace kuma masu inganci don tabbatar da isar kayayyakin abinci na yau da kullun ga al’ummar Falasɗinu a Gaza.

Kotun ta ICJ ta ce Falasɗinawa a Gaza na fuskantar mummunan yanayi na rayuwa kuma yunwa da tsananin rashin abinci na yaɗuwa.

KU KUMA KARANTA: Wakiliyar MƊD ta buƙaci a ƙaƙaba wa Isra’ila takunkuman samun makamai kan kisan kare dangin da take yi a Gaza

“Kotu ta lura cewa Falasɗinawa a Gaza ba barazanar yunwa kawai suke fuskanta ba (…) mummunan fari ma ya kunno kai,” in ji alkalan a cikin umarninsu.

Ƙasar Afirka ta Kudu ce ta buƙaci sabbin matakan a matsayin wani ɓangare na shari’ar da take ci gaba da yi na zargin Isra’ila da kisan kiyashin da take yi a Gaza.

Leave a Reply