Kotun ƙoli ta ce a cigaba da amfani da tsaffin takardun kuɗi na naira 500 da 1000 har zuwa ranar 31 ga Disamba

0
241

A yau Juma’a ne, kotun ƙolin Najeriya ta bayar da umarnin ci gaba da aiki da tsofaffin takardun naira har zuwa ranar 31 ga watan Disamban wannan shekara.

Kotun ƙolin ta umurci babban bankin Najeriya (CBN) da ya bari duka tsofaffin takardun kuɗi na naira da kuma sabbin su riƙa yawo kafada da kafada har zuwa ƙarshen shekara.

KU KUMA KARANTA:Kotun ƙoli ta bayyana shugaban majalisar dattawa, Lawal a matsayin ɗan takarar sanatan Yobe ta Arewa

Duk da umarnin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayar dangane da chanza kuɗaɗen Naira, an yi watsi da su, an kuma ajiye su a gefe saboda wasu dalilai na karya doka da kuma amfani da ikon zartarwa.

Kotun ƙolin ta caccaki shugaba Buhari kan ƙin bin umarnin wucin gadi da ta bayar na ranar 8 ga watan Fabrairu na cewa a bar tsohuwar Naira ta riƙa yawo.

Mai shari’a Emmanuel Akomaye Agim ya bayyana cewa shugaban ƙasar ya nuna rashin biyayya kuma ya kai ga ƙololuwa ta hanyar watsa shirye-shiryen sa na ranar 16 ga watan Fabrairu inda ya amincewa amfani da naira 200 kaɗai.

Leave a Reply