Kotun ƙoli ta bayyana shugaban majalisar dattawa, Lawal a matsayin ɗan takarar sanatan Yobe ta Arewa

4
459

Kotun ƙoli ta tabbatar da Ahmed Lawan, shugaban majalisar dattawa a matsayin ɗan takarar sanata na jam’iyyar APC mai wakiltar Yobe ta arewa.

Jam’iyyar APC ta garzaya kotu tana ƙalubalantar zaɓen Bashir Machina a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a mazabar Yobe ta Arewa.

Jam’iyyar ta ɗage cewa Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawan Najeriya, shi ne sahihin ɗan takarar Sanatan Yobe ta Arewa a babban zaɓe mai zuwa.

A zaman ƙarshe na ɗaukaka karar, lauyan jam’iyyar, Sepiribo Peters ya bayar da hujjar cewa zaɓen fidda gwanin da aka gudanar a ranar 28 ga watan Mayun bara wanda ya haifar da Machina ya saba wa dokar zaɓe ta 2022.

Peters ya ƙara da cewa wani Ɗanjuma Manga da ya gudanar da zaɓen fidda gwanin ba kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar ne ya gabatar da shi ba.

Ya shaida wa kotun cewa jam’iyyar APC ta soke zaɓen fidda gwanin ne saboda wasu kura-kurai da aka samu yayin gudanar da zaben. Ya kara da cewa sauran zaben fidda gwani da aka gudanar a ranar 9 ga watan Yuni jam’iyyar APC NWC ce ta gudanar da ita, kuma ta samar da Lawan a matsayin dan takarar jam’iyyar.

KU KUMA KARANTA:Taƙaddamar Lawan da Machina: Kotun ƙoli ta sake hukunci

Sai dai lauyan Machina, Sarafa Yusuf ya yi addu’a ga Kotun Koli da ta yi watsi da karar da aka shigar kan rashin cancantar a bisa dalilin cewa Shugaban Majalisar Dattawa bai kalubalanci kararrakin ba a kotuna da kuma kananan kotuna.

Ya kuma yi nuni da cewa Manga wanda ya gudanar da zaben fidda gwani inda Machina ya fito, mamba ne a kwamitin da aka nada na NWC domin gudanar da aikin.

Jam’iyyar APC ta garzaya kotun daukaka kara da ke Abuja tana neman ta soke hukuncin da karamar kotun ta yanke wanda ta bayyana Machina a matsayin dan takarar APC a Yobe ta Arewa, sai dai shugabar kotun, Mai shari’a Monica Dongban-Mensem ta jagoranci kwamitin ta tabbatar da cewa an daukaka karan cin zarafin tsarin kotu.

Sai dai a wani hukunci mai rinjaye da aka yanke a ranar Litinin, kotun kolin ta amince da ɗaukaka ƙarar da APC ta shigar kan takarar Bashir Machina. Kotun ƙolin ta bayyana Lawan a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC na jihar Yobe ta Arewa.

4 COMMENTS

Leave a Reply