Kotu ta yanke wa G-Fresh hukuncin ɗauri, EFCC ta gurfanar da Hamisu Breaker

0
523
Kotu ta yanke wa G-Fresh hukuncin ɗauri, EFCC ta gurfanar da Hamisu Breaker
G-Fresh da Hamisu Breaker

Kotu ta yanke wa G-Fresh hukuncin ɗauri, EFCC ta gurfanar da Hamisu Breaker

Daga Jameel Lawan Yakasai

Babbar Kotun Tarayya mai lamba ɗaya da ke Kano ta yanke wa shahararren ɗan TikTok, Abubakar Ibrahim, wanda aka fi sani da G-Fresh, hukuncin daurin watanni biyar a gidan gyaran hali ko biyan tara ta Naira 200,000, bisa samunsa da laifin cin mutuncin Naira.

An gurfanar da G-Fresh a gaban kotun bisa zarginsa da watsa takardun Naira dubu-dubu a cikin wani shago mallakin Rahama Sa’idu da ke unguwar Tarauni, yayin da suke nishadi.

Bayan karanta masa tuhumar, G-Fresh ya amsa laifinsa nan take, lamarin da ya sa alkalin kotun ya yanke masa hukuncin dauri ko tara.

Hukuncin na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomi ke ƙara ɗaukar matakai na hana take hakkin Naira da kuma yada abubuwan da ke rage kimarta a idon al’umma.

KU KUMA KARANTA: Kotu a Kano ta yankewa wasu ‘yan Tiktok 2 ɗaurin shekara 1 a gidan gyaran hali

A wani ɓangaren kuma, Hukumar EFCC ta gurfanar da Mawakin nan wato Hamisu Saidu Breaker a gaban kotun Tarayya karkashin jagorancin mai shari’a Sale Musa Shuaibu bisa zargin cin mutuncin Kudi.

Bayan karanto masa nan take ya amsa, kotun kuma ta yanke masa hukuncin daurin wata biyar ko biyan tarar Naira dubu dari biyu.

An sameshi da watsa takardun Naira dari biyu biyu har na naira dubu talatin a gidan biki a Hadejan Jihar Jigawa.

Leave a Reply