Kotu ta tasa keyar waɗanda ake zargi da kashe dangin tsohon ma’aikacin CBN da wasu a gidan yari

An tsare mutanen biyar da ake zargin na tsawon kwanaki 60 a gidajen gyaran hali da ke Abeokuta. Adekanbi Lekan, Odetola Ahmed da Adeniyi Waheed sune waɗanda ake zargi da kashe ma’auratan Abeokuta da aka kashe a ranar 1 ga watan Janairu, Kehinde tsohon ma’aikacin CBN da matarsa Bukola da ɗansu guda ɗaya tilo Fatinloye, a kotu.

Kotun Majistare II da ke Abeokuta, Jihar Ogun, ta bayar da umarnin kai waɗanda ake zargin gidan yarin, a kuma tsare su tsawon kwanaki 60.

A ranar Laraba ne wata babbar majistare, Esther Idowu, ta ba da umarnin,waɗanda ake zargin, Adekanbi Lekan, Odetola Ahmed da Adeniyi Waheed, an tsare su ne a gidan yari na Oba, yayin da waɗanda ake zargin Fadairo Temitope da Adekanbi Adenike, aka tura su gidan yari na Ibara, dukkansu a Abeokuta.

Mummunan kisan kan ya biyo bayan kashe ma’auratan a ranar 1 ga watan Janairu, maharan sun kuma kona gawarwakin ma’auratan da gidansu da ke rukunin gidajen GRA na Ibara a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

KU KUMA KARANTA:Yadda direba ya kashe mai gidansa ma’aikacin CBN, ya kuma kashe matarsa da ɗansa

Wadanda ake zargin sun kuma ɗaure ɗan ma’auratan ɗaya tilo mai suna Oreoluwa da kuma dan da suke riƙo mai suna Felix Olorunyomi, inda suka jefa su cikin kogin Ogun da ke da nisan kilomita hudu daga gidan.

Yayin da Oreoluwa ya mutu a cikin kogin, ɗan riƙon Olorunyomi, ya tsira.

‘yan sanda sun gabatar da waɗanda ake zargin wata guda da aikata laifin, bayan ‘yan sandan sun kama wasu da ake zargin.

Yayin da ake faretin waɗanda ake zargin a gaban manema labarai a hedikwatar ‘yan sandan jihar da ke Abeokuta, kakakin rundunar ‘yan sandan, Abimbola Oyeyemi, ya ce direban iyalan Mista Adekanbi ne ya shirya aikata laifin saboda a cewarsa iyalan sun ki ƙara masa albashi.

Daga baya rundunar ‘yan sandan ta sanar da kama waɗanda suka sayi motar ma’auratan da aka kashe da ake zargin waɗanda suka kashe su ne suka sace.

A ranar Laraba, wadanda ake zargin sun sayi motar, Owolaja Anuoluwapo da Usman Azeez, an kuma tsare su a gidan yari na Oba na tsawon kwanaki 60.

An gurfanar da dukkan waɗanda ake zargin a gaban kotun bisa tuhume-tuhume 11 da suka haɗa da kisan kai, da haɗa baki wajen aikata babban laifi, cinna wuta, sata, da kuɓuta daga hannun hukuma da dai sauransu.

Za a tsare su na tsawon kwanaki 60 a matakin farko, kamar yadda babban alkalin kotun ya bayyana, har zuwa lokacin da hukumar kula da kararrakin jama’a (DPP) a jihar ta ba da shawarar lauyoyi.


Comments

One response to “Kotu ta tasa keyar waɗanda ake zargi da kashe dangin tsohon ma’aikacin CBN da wasu a gidan yari”

  1. […] KU KUMA KARANTA:Kotu ta tasa keyar waɗanda ake zargi da kashe dangin tsohon ma’aikacin CBN da wasu a gidan yari […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *