Daga; Mustapha Imrana Abdullahi.
BABBAR kotun tarayya da ke kano, ta fara sauraren shedu a tuhumar da ake yi ma Mahadi Shehu ta yada takardun bogi da yunkunrin tunzura jama’a a kan Gwamnatin Jihar Katsina ta hanyar amfani da kafar sadarwa ta yanar gizo.
A Ranar Litinin, 7 ga watan Fabreru na shekarar 2022, Babbar Kotun tarayya da ke Kano ta fara sauraren shedu a cikin karar da Babban Sufeton ‘Yan sandan Najeriya ya shigar yana tuhumar Mahadi Shehu da laifukan ya da takardun bogi da ke dauke da zarge-zargen almundahanar makudan kudade da ake zargin ka iya tunzura jama’a kan Gwamnatin Jihar Katsina a karkashin Gwamna Aminu Bello Masari.
A yayin zaman kotun, jagoran lauyoyin mai kara, Barista Lough, SAN (Babban Lauyan Najeriya), ya gabatar da Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina a matsayin sheda na farko wajen tabbatar da tuhumar da ake yi wa Mahadi Shehu.
Da ya mike domin bada shedar, ya soma da daukar rantsuwar bada sheda cewa zai fadi gaskiya tsagwaronta game da abin da ya sani a cikin wannan shari’ar.
Daga nan sai ya shaidawa Kotun sunansa; Mustapha Muhammad Inuwa, kuma shi ne Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina.
Lauya maigabatar da kara ya tambayi Mustapha Inuwa cewa, ya aka yi ya san Mahadi Shehu ya aikata abin da ake tuhumarsa akai?
Sakataren Gwamnatin ya amsa da cewa; Daraktan Watsa Labaransa mai suna Abdullahi Yar’adua ne ya ankarar da shi a kan wata tattaunawar da ake tuhumar ya yi (a cikin shirin Barka Da warhaka na ranar 2/7/2020) a gidan Radiyon Freedom FM da ke Kaduna, wadda kuma daga bisani ta yi ta yaduwa a gari kamar wutar daji, inda da farko a ciki yake ikirarin cewa jami’an gwamnatin jihar Katsina a karkashin Gwamna Aminu Masari sun yi facaka da kudade sama da Nera Biliyan 24 daga asusun tsaro na jihar.
Ya yi bayanin cewa, hakan ta sanya ya nemi kwafen wannan tattaunawa, shi ma ya saurara da kansa.
Sakataren Gwamnatin ya ce, daga cikin matakan da ya dauka don yin gyara a kan zarge-zargen da Mahadin ke yi, har da kiran taron manema labarai (wanda aka yi a cibiyar ‘yanjaridu ta gidan gwamnati).
Bugu da kari kuma, ya ce ya je har gidan Radiyon na Freedom FM, Kaduna inda har layin waya aka bude, mutane suka rika bugowa, suna yin tambayoyi, kuma a ciki ya musanta zargin yin almundahanar makudan kudaden da Mahadi, ke yadawa.
A cikin shirin, ya ce, ya yi bayani filla-filla dangane da kudaden da wanda ake tuhumar yake zargin wai an wawure inda ya jaddada cewa gwamnatin ba ta ma da wadannan kudin a asusunta na tsaro a jihar.
Bugu da kari, a cikin shirin ya ce, Mahadi, ya ambato sunayen wasu bankuna ciki kuwa har da “Fidelity” wanda sam – sam, gwamnati ba ta da asusun ajiya a bankin, amma Mahadi Shehu, har lambar asusun ya karanto, yana mai ikirarin cewa har ma da takardun yana da su a hannunsa.
Haka kuma, Sakataren Gwamnatin ya ce, ya musanta ikirarin da Mahadi, ya yi na cewa wai gwamnati ta fitar da tsabar kudi har Nera Miliyan 49 don sayen wayar salula guda 12 ga wakilan Majalissar tsaro ta jiha da kuma Nera Miliyan 849, 656, 000 wajen biyan kudaden alawus ga wasu jami’an ‘yan sanda 10, da suke gadi a wata tashar wutar lantarki da ke Lambar Rimi, yana mai ikirarin cewa har a lokacin da yake jawabin suna nan, suna aiki a wurin.
Mai bada shedar na farko, ya fada ma kotun cewa “na 1. wayar salular da Mahadi ke magana akai guda 50 ce aka saya ma ‘yan majalissar zarataswa ta jiha wadda ta kunshi kwamishinoni da masu ba gwamna shawara da sauransu ba Majalissar tsaro ba”.
“Na 2, ya ce jimlar kudin wayoyin (Nokia 3310), da na layukansu, da na tsarin abokan hulda na “CUG” da Kamfanin MTN ya kirkira masu, da cajin jerin lambobin da aka tsara masu da kuma kudin kati na tswon shekara daya duka jimlar Nera Miliyan 2,420,000 sabanin Nera Miliyan 49 da yake ikirari.
A kan batun lambar Rimi kuma, Mustapha Inuwa ya ce, sun iske gwamnatin da suka gada ta tura “yan sanda suna gadi a wurin tun cikin watan 12 na shekarar 2011, lokacin da aka sace wani Bature ma’aikacin kamfanin.
Kuma tun daga lokacin har zuwa watan Ogusta na 2017 da gwamnatin mai ci yanzu ta janye jami’an tsaron, tare da tsaida biyan kudaden saboda masu kamfanin sun dawo, jimlar abin da gwamnatocin biyu suka kashe ita ce Nera Miliyan 12,066,000 ba Miliyan 849,656 000 da yake yadawa ba.
Ya sheda ma Kotun cewa, duk da wannan matakin yin gyaran da gwamnatin ta dauka na yin bayanai tare da fito da sahihan takardun ta, a maimakon Mahadi, ya daina, sai ma ya kara fadadawa, ta hanyar ci gaba da wallafa jerin fayafayan bidiyo, (yana ba su suna) tun daga fitowa ta 1, har zuwa ta dari da wani abu.
Ya tabbatar ma Kotun cewa, irin bayanan da Mahadi, ya rika yi ya taba mutuncin gwamnatin da jami’anta, domin mutane sun sha bugo masu waya daga nan cikin gida da kuma kasashen waje, suna bayyana rashin jindadinsu dangane da abin da Mahadi, ke yada ma duniya cewa shi ne abin da ke faruwa a jihar Katsina.
Hakan ma in ji shi, ya sanya a wani lokaci ‘yayansu kan kasa fita zuwa makaranta saboda guje ma tsangwamar da abokansu ke yi masu bisa yarda da cin zarafin da wanda ake tuhumar ke yadawa a kan iyayensu.
Daga nan ne, sai Alkali ya tambaya cewa ko akwai wani abu da lauya zai nuna a matsayin shedar cewa eh! Lalle Mahadi Shehu ya aikata abin da shedar nasa ya fada?
Lauyan ya amsa cewa ba shakka akwai fayafayan hirar da Mahadi, ya rika yadawa da kwafen jawabin manema labarai wanda Sakataren Gwamnatin ya gudanar da kuma wasu jaridu da suka wallfa labarin.
Sai dai kuma, da aka nemi ya kawo su, Barista Lough ya ce sun manta ba su zo da su ba (abin da ya fusata ran mafi yawancin ‘yankallo), amma ya roki Kotun da ta ba su wata rana da za su kawo abin nunin shedar.
A yayin da Alkalin Kotun Mai shari’a A.A Liman, ya waiwayi jagoran Lauyoyin wanda ake tuhumar, Barista A.I Abubakar, ya amince da wannan bukatar, sai ya daga zuwa ranakun 28/2, da kuma 3/1/2022, domin ci gaba da sauraren shedun maigabatar da kara tare da cewa wanda ake tuhumar ya ci gaba da zama a kan beli har zuwa ranar da za a dawo kotu.
Sai dai wani abin da aka lura da shi a wannan karon shi ne, wanda ake tumar, Mahadi Shehu, dan Najeriya, dan asalin jihar Katsina, haifaffen kofar sauri, ya zo kotun tangaram, yana sanye da wando da taguwarsa mai gajeren hannu, farare wadanda da aka fi sanin shi da su, da ‘yar farar hularsa da kuma tabarau.
Kusan in baya ga takunkumin korona wanda kowa a cikin kotun yana na sanye da shi, bai zo da sandunan guragu, ko ya dauro janjami, ko wani abu da ya saba ma al’ada ba.
Hasali ma a wannan karon, akawun kotun na kiran sunasa a matsayin wanda ake tuhuma, sai ya yi zambur, ya mike, ya nufi akwatin da a kan saka wanda ake tuma, ya tsaya kyam, ya kuma yi kasake yana jin dukkan shedar da Dokta Mustapha Inuwa yake badawa, gaba da gaba dangane da abin da ake zarginsa da wallafawa.
“kowa ya debo da zafi bakinsa”.