Kotu ta ayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano

1
342

Daga Ibraheem El-Tafseer

Kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamnan Kano ta soke nasarar Abba Kabir Yusuf, a matsayin halastaccen gwamna.

Sannan ta ayyana ɗan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya ci zaɓen da ya gudana a ranar 18 ga watan Maris ɗin 2023.

Jam’iyyar APC ce ta shigar da ƙara a gaban kotun, tana ƙalubalantar nasarar Abba Kabir.

Kotun ta bayyana wannan hukunci ne ranar Laraba, ta hanyar manhajar Zoom, cikin wani tsattsauran yanayin matakan tsaro a birnin Kano.

Mai shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay, ita ce shugabar kotun wadda ta jagoranci alƙalan kotun guda uku.

Kotun ta ce ta yanke wannan hukunci ne bisa hujjar cewa an yi aringizon ƙuri’u har 165,633, waɗanda aka gano ba su da sitamfi da kuma kwanan wata a cikin ƙurin Abba Kabir.

KU KUMA KARANTA: Ganduje ba zai iya kallon idona kai tsaye ba, ni ubansa ne a siyasa – Kwankwaso

Tun farko a watan Maris ɗin 2023, hukumar zaɓen ta ce ɗan takarar NNPP, Abba Kabir Yusuf ya ci zaɓen ne da ratar ƙuri’a 128,900.

Abba Kabir Yusuf, in ji INEC ya samu ƙuri’u mafi rinjaye da suka kai 1,019,602, inda Nasiru Yusuf Gawuna da ke biye da shi, ya samu ƙuri’a 890,705.

Alƙalan kotun sun umarci hukumar zaɓe ta INEC ta janye shaidar cin zaɓen da ta bai wa Abba Kabir Yusuf, tare da gabatar da ita ga Nasiru Yusuf Gawuna.

Lauyan jam’iyyar NNPP, Bashir Muhammad Tudun Wuzirci bayan fitowa daga kotun, ya ce hukuncin ya zo musu da mamaki, wanda in ji shi bai kamata a ce an yi haka ba.

Ya ce amma akwai kotuna na gaba, kuma suna tabbatar da cewa idan sun je gaba, za su warware abin da ya ƙira “wannan surkullen da aka yi wanda bai kamata a yi ba”.

A cewarsa, ko da wasa ba su yarda da wannan hukunci ba, don haka za su yi shawara da mutanen da suke wakilta “kuma in Allah ya yarda za mu ɗau mataki na gaba”.

Barista Bashir Tudun Wuzirci ya ce irin haka ta faru a jihar Osun, amma kotun ɗaukaka ƙara ta zo ta warware kuma Kotun Ƙoli ta tabbatar da cewa abin da tirabunal ta yi ba daidai ba ne.

1 COMMENT

Leave a Reply