Kasuwanci: Aljeriya za ta haɗa gwiwa da Masarautar Kano

1
498

Shugaban ƙasar Aljeriya, Abdulmajid Tebboune, ya bayyana aniyarsa ta haɗa kai da mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, kan inganta hulɗar da ke tsakanin ƙasarsa da jihar Kano, ta hanyar kasuwanci da musayar ilimi.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baquncin mai martaba sarkin Kano a fadar shugaban ƙasa da ke birnin Algiers, jim kaɗan bayan ya isa ƙasar Algeria domin halartar taron ƙasa da ƙasa kan rayuwa da zamanin Imam Al-Maghili bisa gayyatar da shugaban ƙasar Aljeriya ya yi masa.

Ya ce alaƙar ƙasarsa da Najeriya ta ginu ne a kan ƙwararan hujjoji na tarihi, bayan zaman Imam Al-Maghili a Kano, inda ya bayyana ƙudurinsa na tallafawa duk wani shiri da zai inganta haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu, musamman ta hanyar kasuwanci da musayar ilimi.

A cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labarai na Masarautar Kano, Abubakar Balarabe Ƙofar Naisa ya fitar, ya bayyana cewa shugaba Tebboune ya yi alƙawarin kara wa ɗaliban Najeriya guraben ƙaro karatu a fannonin shari’a, kimiyya da kuma koyon sana’o’i.

Tun da farko, Sarkin Kano ya bayyana cewa alaƙar tarihi da ta daɗe a tsakanin Kano da Aljeriya ta samo asali ne daga ziyarar da malamin addinin Musulunci kuma masanin falsafa ɗan ƙasar Aljeriya Imam Abdurrahman Al-Maghili ya kai Kano a karni na 15.

1 COMMENT

Leave a Reply