Kamfanin Jaridar Neptune ya horar da ‘yan jarida sanin makamar aiki a Yobe
Daga Idris Umar, Zariya
Kamfanin Neptune Network Nigeria Limited (NNNL), mai buga jaridar Neptune Prime a Turanci da Hausa, tare da tallafin kungiyar ‘Yobe First Movement (YFM), za su gudanar da Taron Horarwa na Yanki kan dabarun yada labaru, wanda zai gudana a garin Potiskum, dake jihar Yobe.
Wannan taro ya gudanane ƙarƙashin Mawallafin kuma/Shugaban Kamfanin NNNL, Malam Hassan Gimba, inda ya ce, taron ya karfafa kwarewa da sanin makamar aikin jarida don fadakar da jama’a da kuma yadda ake amfani da shafukan sada zumunta don isar da sako.
horas ya baiwa mahalarta taron dabaru da samun kwarewar rubuce-rubucen da suka shafi abubuwan da suka faruwa na al’ammuran yau da kullum, wadanda suka shafi manufofin gwamnati.
KU KUMA KARANTA:Gwamnan Yobe ya ziyarci aikin magudanar ruwa a Damaturu
Horon, wanda ya kunshi kungiyoyin al’umma 20 daga kananan hukumomin Potiskum, Fika, Fune, da Nangere dake jihar Yobe, wanda za gudanar a garin Potiskum.
Har wala yau wannan horon zai amfanar a matsayin samfuri na farko, wanda masu shirya taron za su wajen zakulo karin wasu kungiyoyi daga sauran sassan jihar, nan gaba.
Kwararrun da ake sa rai zasu ci gaba da gudanar da ayyukan bayar da horon sun hada da Dokta Ahmed Mohammed Bedu, kwararre a fannin sadarwa, kuma tsohon shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa a jihar Yobe (NUJ), kuma malami a Jami’ar Maiduguri; Dokta Saleh Mari Maina, kwararren dan jarida kuma malami a Cibiyar Ci Gaba mai Dorewa, Jami’ar Abuja da Jami’ar Bayero (BUK) da Jami’ar Baba Ahmed, duka a Kano.
Sauran su ne Malam Abubakar Ahmed, tsohon mataimakin darakta a Kamfanin Dillancin Labaru (News Agency of Nigeria- (NAN), da Dokta Furera Bagel, malama a fannin ilimin harshe a Jami’ar Jihar Bauchi.









