Gwamnan Yobe ya ziyarci aikin magudanar ruwa a Damaturu
Daga Ibraheem El-Tafseer
Gwamnan jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni ya duba aikin magudanar ruwa da ake birnin Damaturu fadar gwamnatin jihar Yobe.
Gwamnan ya umurci ’yan kwangilar da ke gudanar da aikin da su ƙara saurin aiwatar da aikin kafin sauƙar ruwan sama.
“Ya kamata a kammala wannan aikin kafin a fara damina.
“Kada a jinkirta don gudun ka da ruwan sama ya koma gida da kuma mamaye gidajen mutane” Gwamnan ya yi gargadin.
Gwamna Buni ya ce zai ci gaba da sanya idanu kan aikin har sai an kammala aikin.
KU KUMA KARANTA: Kamfanin Neptune Prime zai horar da ‘yan jaridu kan yaɗa labarai ta kafafen sada zumunta a Yobe
Ya kuma ba da tabbacin gwamnati ta himmatu wajen sauƙe nauyin da ya rataya a wuyanta na gaggauta kammala aikin.
Idan dai ba a manta ba gwamnatin jihar Yobe ta bayar da kwangilar gina magudanan ruwa a garuruwan Buni Yadi da Damaturu domin duba ambaliyar ruwa da kuma girbe ruwan damina domin bunkasa noman rani.