Jami’an tsaro sun kai samame gidan Tukur Mamu da ke Kaduna

0
371

Jami’an tsaro, waɗanda ake kyautata zaton jami’an hukumar ‘yan sandan farin kaya ta DSS ne a Najeriya sun kai samame gidan Tukur Mamu, mutumin da ke shiga tsakani da ‘yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasa na Kaduna.

Wasu mazauna unguwar sun tabbatar wa da BBC cewa jami’an tsaron sun isa gidan ne da ke Kaduna a motoci kimanin 10 da sanyin safiyar yau Alhamis, inda suka yi awon gaba da wasu kayyayaki.

KU KUMA KARANTA: An kama Tukur Mamu, mai shiga tsakani don ceto fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Tukur Mamu dai shi ne mutumin da ke shiga tsakanin ‘yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasa a Kaduna da kuma iyalansu domin kubutar da su. Fasinjojin da aka kubutar daga hannun ‘yan bindigar kan fara zuwa ofishinsa da farko, kafin su hadu da iyalansu.

A jiya ne dai ‘yan sandan kasa da kasa na kasar a Masar suka kama Tukur Mamu a filin jirgin saman a birnin Al-khahira, lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya.

Hakan na zuwa ne bayan rundunar soji, da fannin shari’a sun bukaci abokan huldarsu na kasashen waje su dawo da Mamu gida domin amsa tarin tambayoyin da jami’an tsaron Najeriya ke son ya amsa musu, masu alaka da batutuwan tsaro da kasar ke fama da su.

Leave a Reply