INEC ta bayyana Tunibu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2023

0
384

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

KU KUMA KARANTA: Asiwaju Bola Tinubu Ne Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin Jam’iyyar APC Da Kuri’u 1271

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen a asubar Laraba, 1 ga Maris, 2023.Tinubu ne ya lashe zaɓen bayan samu ƙuri’u 8,794,726.

An bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan ya cika dokar da ake bukata, bisa ga tsarin zaɓe. Dan takarar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya samu ƙuri’u 6,984,520, Peter Obi na jam’iyyar Labour Party (LP) ya samu ƙuri’u 6,101,533 Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya samu kuri’u 1,496,687.

Leave a Reply