No menu items!

Sample Page Title

Date:

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu mutane biyu bisa zargin shirin auren jinsi a jihar.

Kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai cewa mutanen biyu suna hannunsu, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.

A cewarsa, “A cikin wani faifan bidiyo, an ga samarin biyu mai suna Khalifa da Abubakar suna ƙoƙarin sumbatar juna a yayin wani biki, wanda ake zargin alama ce ta auren su”.

Sai dai waɗanda ake zargin sun musanta zargin cewa taron bikin ranar haihuwa ne ba bikin aure ba kamar yadda hukumar Hisbah ta yi iƙirari.

KU KUMA KARANTA: Hisbah ta kama mata 15 da suka halarci bikin ‘yan luwaɗi a Kano

Khalifa, ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, ya ce sun shirya bikin zagayowar ranar haihuwarsa, sai abokinsa Abubakar ya ba shi biredi a bakinsa, ya bi bakinsa ya gutsura.

Daurawa ya ce mutanen biyu suna hannunsu, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kan wannan zargi da ake musu na auren junansu.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

1 COMMENT

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...