Hukumar EFCC ta gano naira biliyan 30 a wajen Betta Edu

0
134

Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC, ta ce ta gano Naira biliyan 30 a wajen ministar ma’aikatar jin kai da aka dakatar, Betta Edu.

Haka kuma ta ce tana gudanar da bincike kan wasu asussan banki 50 duka a cikin badaƙalar kuɗaɗe da aka yi a ma’aikatar.

Shugaban hukumar ta EFCC, Ola Olukoyede, ne ya bayyana haka, inda ya ce akwai buƙatar a kafa kotuna na musamman waɗanda za su lura da shari’oin zargin cin hanci.

Olukoyode ya ce kuɗaɗen da aka kwato suna cikin asusun gwamnatin tarayya a halin yanzu.

EFCC dai na gudanar da binciken badaƙalar da aka samu a ma’aikatar jin kai da ta shafi ministar da aka dakatar, Betta Edu, da tsohuwar ministar ma’aikatar, Sadiya Umar-Farouq, da kuma Halima Shehu, shugabar hukumar ba da tallafin dogaro da kai ta ƙasa NSIPA.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta bayar da umarni EFCC ta tsare Emefiele

A watan Janairu ne dai shuganubu ya dakatar da Edu sakamakon badakalar kuɗaɗe a ma’aikatar.

Daga nan ne EFCC ta kira ta domin amsa tambayoyi bayan fitar wata takarda da ta nuna cewa Betta ta ba da umarnin biyan sama da naira miliyan 585 cikin asusun ajiyar wani mutum, lamarin da ya saɓa da ƙa’idar aiki.

A cikin wata wasiƙa da aka yi zargin ministar ta sanya hannu, Betta ta umarci babbar akantar Najeriya, Oluwatoyin Madein ta zuba kuɗi cikin asusun wata mai suna Oniyelu Bridget, a matsayin tallafi ga ƙungiyoyin mutane masu rauni a jihohin Akwa Ibom da Cross River da Lagos da kuma Ogun.

Sai dai babbar akantar ta yi bayanin cewa, ko da yake ofishinta ya karɓi wannan buƙata daga ma’aikatar jin ƙai, amma bai yi abin da aka nema ba.

Betta Edu, ‘yar shekara 37, wadda ita ce matashiya mafi ƙaranci shekaru a jerin ministocin Tinubu, daga bisani ta ce ƙulle-ƙulle ne kawai ake yi don a ɓata mata suna, ta ƙara da cewa ba za ta yi almundahana da duniyar gwamnati ba.

Leave a Reply