Gwamnatin Yobe za ta mayar da kwale-kwalen Dufuna mai shekaru 8,000 zuwa cibiyar yawon buɗe ido

0
173

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnatin jihar Yobe na shirin mayar da tsohon kwale-kwalen Dufuna ya zama wurin yawon buɗe ido a jihar.

A wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, ta ruwaito kwamishinan harkokin cikin gida, yaɗa labarai da al’adu, Honorabul Abdullahi Bego, yana cewa burin gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni shi ne ceto tare da dawo da kwale-kwalen Dufuna mai shekaru 8,000 da aka gano. Kuma an tono shi a cikin shekarar 1998 kuma a sanya shi a matsayin babban abin jan hankali a cikin jihar.

Bego ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da sabon Darakta-Janar na Hukumar Kula da Gidajen Kayayyakin Tarihi (NCMM), Mista Olugbile Holloway, da wasu ma’aikatan gudanarwarsa a Abuja.

KU KUMA KARANTA: Ɗan yawon buɗe ido na Amurka ya mutu bayan faɗowa daga Rufin otal mai tsayi 100

A cewarsa, kwale-kwalen ya samo asali ne tun fiye da shekaru 8,000 da suka gabata, kuma an ce shi ne jirgin ruwa mafi daɗewa a yankin kudu da hamadar Sahara, wanda ke nuna sha’awar gwamnati ta mayar da shi ɗaya daga cikin wuraren yawon buɗe ido a jihar.

Leave a Reply