Gwamnatin Najeriya ta ƙayyade mafi ƙarancin shekaru na shiga jami’a
Daga Jameel Lawan Yakasai
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta ƙayyade mafi ƙarancin shekaru da ɗalibai za su iya samun gurbin karatu a manyan makarantu zuwa shekara 16.
Alausa ya yi wannan bayani ne a Abuja a yau Talata yayin taron tattaunawa kan manufofi da dokoki da hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare, JAMB, na 2025 ta shirya.
KU KUMA KARANTA: Za a fara amfani da sabuwar manhajar ilimi a watan Janairun 2025 – Ministan Ilimi
“Wannan matakin manufofi zai kawo daidaito tsakanin shekarun balaga da kuma girman jiki na shiga jami’a. Mun ƙayyade shekara 16 kuma babu canji daga haka,” a cewar sa.
Ya gargadi makarantu da kada su nemi kauce wa wannan doka ta hanyar canza shekarun ɗalibai, yana mai jaddada cewa duk wani yunƙuri na irin haka zai fuskanci hukunci









