Gwamnatin Najeriya ta ƙara ranakun hutun ƙaramar Sallah

Gwamnatin tarayya ta amince da ranar Alhamis, 11 ga Afrilu, 2024, a matsayin kari a kan ranakun hutun sallar Eid-El-Fitr ta bana.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Dr Aishetu Gogo Ndayako, babban sakatare na ma’aikatar harkokin cikin gida da ya ba da izini a safiyar yau Talata.

Sanarwar ta rawaito Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya nanata kudurin shugaba Bola Ahmed Tinubu na samar da zaman lafiya da wadata a Najeriya domin kowa ya samu ci gaba.

“Mai girma ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, yayin da yake taya al’ummar musulmi murnar kammala wata guda na ibada, ya nanata ƙudurin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu (GCFR) na samar da kasar Najeriya lafiyaiya da wadata ga kowa da kowa ya samu ci gaba. ,” in ji sanarwar.

KU KUMA KARANTA: Ba a ga watan sallah a Najeriya ba

Tun da fari dai, gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Talata da Laraba 9 da 10 ga Afrilu, 2024, a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bukukuwan Sallah.

Sai dai kuma rashin ganin jinjirin wata a jiya Litinin, lamarin da ya sa aka ayyana ranar Laraba a matsayin Eid-el-Fitr.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *