No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gwamnatin Najeriya ta ƙara kuɗin wutar lantarki ga rukunin kwastomomin da suka fi samun wuta, waɗanda ake ƙira Band A customers a turancin Ingilishi.

Band A su ne rukunin kwastomomi da suke samun wutar lantarki ta aƙalla awa ashirin a kowace rana.

A yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja ranar Laraba, shugaban hukumar da ke sanya ido kan harkokin lantarki ta Najeriya (NERC), Musliu Oseni ya ce yanzu kwastomomin za su riƙa biyan ₦225 kan kowane kilowat na wuta da suka sha maimakon ₦66 da suke biya a yanzu.

KU KUMA KARANTA: Ministan Lantarki na Najeriya ya yi barazanar ƙwace lasisin kamfanonin rarraba wuta

Oseni ya ce waɗannan kwastomomi su ne kashi 15 na mutum miliyan 12 da suke amfani da lantarki a faɗin Nijeriya.

Ya ƙara da cewa wannan sabon ƙarin kuɗin lantarki ba zai shafi sauran kwastomomi ba.

A watan Janairun da ya gabata, hukumar NERC ta ce gwamnatin Nijeriya za ta kashe kimanin N1.6 tr domin biyan tallafi kan kuɗin lantarki da za a bai wa ƴan ƙasar a shekarar 2024.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...