Hukumar sadarwa ta ƙasar Ghana NCA, ta sanar da rufe gidajen rediyo saboda gudunmuwar da suke bayarwa wajen ruruta wutar rikicin ƙabilanci da yaƙi ci, yaƙi cinyewa a yankin Bawku na jahar maso gabashin ƙasar Ghana.
Al’umman yankin Bawku na jahar maso gabashin ƙasar sun nuna damuwarsu matuƙa bisa matakin da gwamnati ta ɗauka na rufe gidajen rediyon da suka haɗa da Gumah FM, Bawku FM da Souce FM tare da Zahra FM, inda suke cewa, hakan zai hana su samun labarai tare da wasu abubuwan da za su amfanar da su cikin harkokinsu na yau da kullum.
A wani jawabin da darektar sashen kula da harkokin kamfanoni a hukumar sadarwa ta ƙasa NCA, Nana Defie Badu ta gabatar bisa matakin rufe gidajen rediyo, tace;
“hukumar tsaro ta ƙasa ta National Security bayan bincike mai zurfin gaske da ta aiwatar, ta tabbatar da cewa, waɗannan gidajen rediyo suna ba da gudunmuwa wajen kawo rashin zaman lafiya a yankin Bawku don haka ta ɗauki wannan mataki da doka ta ba ta damar ladabtar da masu yaɗa labarai har in suka aikata ba daidai ba. Muna aiki tare da hukumar tsaro ta ƙasa ne domin ganin an samu zaman lafiya a yankin”
An yi asarar rayuka masu yawa da dukiyoyi kazalika dubban jama’ar yankin sun yi ƙaura daga Bawku zuwa kudancin kasar domin neman mafaka.
Gidajen rediyo huɗun sun nuna rashin jin daɗinsu bisa wannan mataki.
A hirarsa da muryar Amurka, Nurudeen Gumah darektan gidan rediyo ta Gumah FM ya ce;
“kafin hukumar NCA ta rufe gidajen rediyo ya kamata ta rubuta mana wasiƙa ta nuna mana dalilin hakan tare da baiwa gidajen rediyo wa’adi yaso mu shirya in kuma muna da wani jawabi ne mu gabatar amma kai tsaye wasu dakarun soja suka iso a gidajen rediyon tare da rufe su da kuma yin awon gaba da naurorin transmitter ɗinsu. Babu wanda ya tuntuɓe mu kuma babu wanda ya bamu takarda cewa ga matakin da za’a ɗauka a kanmu, nan take aka kawo takarda kuma rufe gidajen ya biyo baya”.
A bayaninsa, Umar Sanda Ahmad ɗaya daga cikin masu sharhi kan sha’anin tsaro a Ghana yace wannan mataki ya dace sosai saboda har in an shirye shiryen da tashoshin suke gabatarwa na ba da gudunmuwa wajen rura wutar rikici a yankin dole ne hukumomi su hana hakan. Umar Sanda ya ba da misali da abinda ya haifar da rikicin ƙabilanci a ƙasar Rwanda bayan wasu kalaman tunzura jama’a da aka gabatar a rediyo inda hakan zai iya faruwa adon haka matakin gwamnati ya yi daidai.
Rediyo na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ba da gudunmuwa wajen ƙarfafa Demokraɗiyyar amma kuwa har in zai janyo rikici to rufeshi shi ne mafi alheri saboda Demokraɗiyyar baya hura wutan rikici inji Shariff Abdul Salam mai sharhi kan al’amurran yau da kullum.
KU KUMA KARANTA:Shugaban Ghana ya sallami Ministan Kuɗi, Ken Ofori-Atta, daga aiki
Kafin rufe waɗannan gidajen rediyo guda huɗu, Majalisar wanzar da zaman lafiya ta ƙasa ta buƙaci gwamnati ta rufe biyu daga cikin gidajen rediyo huɗu da aka rufe, wato Bawku FM da Souce FM bisa gudunmuwar da tace suke bayarwa wajen assasa wutar rikicin ƙabilanci a yankin.
Gwamnatin Ghana ta sha rufe gidajen rediyon saboda rashin sabunta lasisi amma ba saboda matsalar tsaron ƙasa ba kamar matakin da ta ɗauka kan waɗannan gidajen rediyo huɗu da ke yankin Bawku.
Tuni dai gidajen rediyon suka miƙa takardar buƙatar su ga gwamnati domin ganin an samu nasarar watsa shirye-shiryen da ake buƙata maimakon rufe gidajen rediyon.